Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana kamfanonin taba sigari a matsayin manyan masu gurbata muhalli da kuma haifar da dumamar yanayi a duniya.
Hukumar ta zargi kamfanonin da haifar da sare dazuka da mamaye filayen da ake matukar bukata da kuma ruwa a kasashe matalauta da ake bukatar su domin yin noma da samar da abinci, yayin da suke fitar da robobi tare da sinadare masu guba da kuma miliyoyin tan na sinadarin ‘carbon dioxide’.
Rahotan Hukumar da aka fitar a wannan Talatar a daidai lokacin da ake bikin ranar yaki da shan taba ta duniya, ya bukaci dorawa kamfanonin sarrafa tabar alhakin tsaftacce muhallin da suke gurbatawa.
Hukumar ta ce kamfanonin sun yi sanadiyar asarar bishiyoyi miliyan 600 a duniya, yayin da ake amfani da eka dubu 200 na filaye wajen noma tabar da tan biliyan 22 na ruwa, a daidai lokacin da kamfanonin ke sanadiyar fitar da gurbatacciyar iskar ‘carbon dioxide’ tan miliyan 84 a duniya.
A wani labarin na daban shugabannin Kasashen Turai sun yanke hukuncin haramta sayen kashi biyu bisa uku na man kasar Rasha, a wani yunkuri na ci gaba da matsin lamba akan tattalin arzikin kasar, yayin da sojojin Rashar ke ci gaba da kai munanan hare hare a Gabashin Donbas dake Ukraine.
Shugaban majalisar Turai Charles Michel ya bayyana matakin a matsayin tsatsauran mataki akan kasar dan ganin ta kawo karshen yakin.
Shugabannin kasashe 27 dake kungiyar Turai sun shirya taron ne domin cimma yarjejeniya ta dogon lokaci, duk da korafin da kasar Hungary tare da makotan ta ke yi sakamakon dogara da makamashin na Rasha.
Yarjejeniyar shugabannin ta kuma kunshi aikawa Ukraine euro biliyan 9 cikin gaggawa domin inganta harkokin kudaden kasar tare da fitar da babban bankin Rasha na Sberbank daga cikin shirin SWIFT na musayar kudade tsakanin bankunan duniya, tare da haramta ayyukan kafofin yada labaran kasar guda 3 da kuma sanya wasu mutane cikin kundin masu taimakawa wajen aikata laifuffukan yaki.
Kafin cimma wannan matsaya, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana takunkumin cinikin man a matsayin mafi radadi, yayin da ya roki kasashen Turan ad suyi watsi da makamashin Rashar domin samarwa kansu yanci.