Jarirai bakwaini 36 a asibitin Al Shifa na Gaza na cikin yanayin mutu kwakwai rai kwakwai, a cewar ma’aikatan kiwon lafiya, waɗanda suka suka ce babu wata tabbatacciyar hanyar taimaka musu duk da kokarin da Isra’ila ta yi na samar da kwalaben da za a kwashe su a ciki.
Uku daga cikin jarirai bakwaini 39 sun riga sun mutu tun lokacin da janareton babban asibitin Gaza ya daina aiki saboda ƙarewar fetur a karshen mako, wanda shi ne ke samar da wutar lantarkin da ke sa wa kwalaebn ajiye su suke aiki.
An yi sa’a har yanzu 36 da ba su mutu, ba mu rasa ko daya daga cikinsu a cikin dare daya ba,” Dr Ahmed El Mokhatallali, wani likitan tiyata, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho daga Al Shifa. “Amma duk da haka hadarin yana da yawa … za mu iya rasa su.”
1417 GMT — Asibitoci 25 cikin 35 na Gaza sun daina aiki saboda yaƙin Isra’ila – Hamas
Wani jami’in Hamas ya ce harin bama-bamai da Isra’ila ta kai a Gaza ya sanya 25 daga cikin asibitoci 35 na yankin da aka yi wa ƙawanya sun daina aiki.
Osama Hamdan wani jami’in kungiyar Hamas da ke birnin Beirut, ya shaida wa taron manema labarai a babban birnin kasar Labanon cewa “Hare-haren Isra’ilan sun kuma lalata gine-ginen gwamnati 94 da makarantu 253.”
1420 GMT — Hezbollah ta ce ta raunata sojojin Isra’ila a kan iyaka
Kungiyar Hezbollah ta Lebanon ta ce ta kai hari ga sojojin Isra’ila a sansaninsu da ke kusa da kan iyaka inda ta raunata su.
Kungiyar ta Hezbollah na taya Hamas yakin da take yi da Isra’ila.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare Gaza inda ta kashe sama da mutum 11,200.
0935 GMT — An binne gawawwaki 179 a cikin kabari guda a harabar asibitin Gaza
Daraktan asibitin Gaza mafi girma a ranar Talata ya ce mutum 179, daga ciki har da jarirai da marasa lafiya wadanda suka mutu a dakin kula da marasa lafiya an binne su a cikin kabari guda a harabar asibitin.
“An tilasta mana rufe su a kabari daya,” in ji daraktan Asibitin Al-Shifa Mohammad Abu Salmiyah inda ya ce akwai jarirai bakwai da marasa lafiya 29 wadanda ke dakin marasa lafiya masu tsananin bukatar kulawa na daga cikin wadanda aka binne.
Source: TRThausa