Kakakin Rundunar Jami’an ’Yan Sandan Najeriya, Frank Mba ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa wadanda ake zargin sun sace dattijon sun tsare shi tsawon kwana takwas, alhali yana fama da rashin lafiya.
A cewar kakakin Jami’an , bayan tattaunawa mai tsawo, an biya masu garkuwar kudin fansa Naira miliyan 10, amma maimakon su sake shi, sai suka kashe shi.
“A kwana 30 da suka gabata, Jami’an ’yan sanda sun samu gagarumar nasarar cafke mutum takwas kan zargi da taka muhimmiyar rawa a garkuwa da kuma kashe mahaifin tsohon gwamnan.
“Wadanda ake zargin, dukkansu — inda kadan daga cikinsu — ’yan kauye daya da marigayrin a Karamar Hukumar Bokkos,” inji shi.
A cewar Kakakin Jami’an babban wanda ake zargin, wanda kuma ya jagoran ci rabon kudin fansar, shi aka far cafkewa, sannan ya ya tona asirin ragowar.
Mba ya ce an kuma cafke mutum uku tun ranar 28 ga watan Agusta a wani gari da ke tsakanin iyakar Jihar Nasarawa da Jihar Taraba bayan da aka shafe watanni ana neman su.
Har wa yau, Mba, ya ce an kamo wasu wadanda ake zargi da laifin saye da sayar da makamai ga masu aikata laifuka a jihohi daban-daban, bayan da jami’an leken asiri suka kai wani samame, bayan samun bayanan sirri.
Mba ya ce an kwato bindigogi kirar AK-47 guda 26, alburusan AK-49 da kuma alburusai kananan bindigogi 14 daga hannun wadanda aka cafke.
Ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotu bayan an kammala bincike.