Kamar yadda ministan lafiya na jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Namaky ya tabbatarwa da manema labarai a tehran babbar birinin jamhuriyar musulunci ta Iran, ya tabbatar da cewa masana kimiyyar Iran din sunyi nasarar samar da allurar rigakafin korona wacce tasirin ta yafi na sauran da aka samar a baya a sauran kasashen duniya.
Tare da matsin takunkumin tattalin arzuki dana kayan magani da amurka ta kakabawa kasar ta Iran amma masana kimiyyar ta sun iya samar da allurar rigakafin ta korona akan lokaci kuma bisa yanayi mai kyau da tsafta, sa’annan maganin baya da wata matsala kamar yadda ministan ya tabbatarwa da m,anewa labarai.
Domin taabbatar da ingancin allurar rigakafin ta korona an fara gabatar da ita a kan jagoran juyin juya halin musulunci na Iran ne, Jagora sayyid Ali Khamne’e.
Ma’aikatar lafiya ta Iran ta nuna farin cikin ta kuma ta bayyana wannan nasara a matsayin manyan manyan nasarorin ta ta cimma sa’annan ta bada izinin amfani da rigakafin koronar wanda kamfanin ”Barekat” suka samar a fadin kasar ta jamhuriyar msulunci ta Iran.
Dangane da ko kasar Iran zata saida ma kasashe masu bukata allurar rigakafin data samar ministan ya kada baki yace ba za’a sayar da ko guda daya ba har sai an yima gabdayan Iraniyawan domin rayuwar Iraniyawan itace mafi muhimmanci a sahun farko.
Kasar Iran dai tana cikin kasashen da amurka ta kakaba musu manyan takunkuman tattalin arziki dama kayan magunguna tsawon kusan shekaru takwas, bisa neman ko Iran din zata nemi sulhu idan abubuwa suka wuyatar mata amma abin mamaki kasar ta iya shanye takunkuman ba tare da tayi kasa a gwuiwa ba.
Gwamnatin shugaba joe biden na amurka wacce ake ma kallon mai sassaucin ra’ayin tada zaune tsaye ce amma bata sassautawa Iran din ba sai ma cigaba daga inda gwamnatin trump ta tsaya.