Harin da Isra’ila ta kai kwanakin baya a Asibitin Al Shifa ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 500.
0749 GMT — Manyan motoci 187 dauke da kayan agaji sun isa Gaza
Kugiyar agaji ta Palestine Red Crescent Society ta ce tawagar manyan motoci 187 dauke da kayan agaji ta isa yankin Gaza da aka yi wa kawanya daga Mashigar Rafah.
A wata sanarwa, ta ce tawagarta ta karbi manyan motoci 187 dauke da kayan agaji daga kungiyar agaji ta Egyptian Red Crescent, tana mai cewa ta karbi motoci 81 ranar Laraba yayin da ta karbi motoci 106 a yau Alhamis, da kuma motoci biyar na daukar marasa lafiya daga Kuwait.
Ta kara da cewa duk da hana shigar da fetur yankin, motocin na dauke da magunguna da abinci da ruwa da sauran kayan agaji.
0600 GMT — Isra’ila ta sake kai harin bama-bamai a Asibitocin Al Shifa da Al Nasr na Gaza
Jiragen yakin Isra’ila sun yi luguden wuta a Asibitin Al Shifa da Asibitin Yara na Al Nasr da ke Gaza.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Falasdinawa WAFA, Isra’ila ta harba rokoki a Asibitin Al Shifa, inda dubban majinyata da ‘yan gudun hijira suke samun mafaka.
Harin da jiragen suka kai kusa da Asibitin Yara na Al Nasr da ke yammacin Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa uku da jikkata da dama.
0509 GMT — Amnesty International ta nemi Isra’ila ta kawo karshen ‘rashin imani’ a kan Falasdinawa a Gabar Yammacin Kogin Jordan
Hukumomin Isra’ila suna kara yin amfani da tsarin daure Falasdinawa ba bisa ka’ida ba a Gabar Yammacin Kogin Jordan kuma sun ki yin bincke kan zargin gallazawa da kashe wadanda suka daure, a cewar kungiyar kare hakkin Dan’adam ta Amnesty International a ranar Laraba.
A yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare Gaza, Amnesty International ta ce ana gallaza wa fursunoni Falasdinawa da take hakkokinsu da daure su ba bisa ka’ida ba.
“Kazalika sun bullo da wani tsari na daure mutane cikin ‘gaggawa’ da ya ba su ikon musguna wa Falasdinawa da nuna musu rashin imani,” in ji kungiyar a sakon da ta wallafa a shafin X.
Ta jaddada kiran da ta yi na sakin fursunoni nan-take.
Alkaluma sun nuna cewa Isra’ila ta kashe Falasdinawa 10,600, galibinsu fararen-hula.
0430 GMT — Sanatan Amurka ya ce fararen-hula da ake kashewa a Gaza ‘sun yi yawa’
Wani dan Majalisar Dattawan Amurka ya ce yana da “muhimmanci” Isra’ila ta rika yin taka-tsantsan wurin kai hare-hare Gaza domin ta rage kisan fararen-hula.
“Ina gani fararen-hula da ake kashewa sun yi matukar yawa kuma akwai bukatar a yi taka-tsantsan,” a cewar Chris Murphy, Sanata na jam’iyyar Democrat kuma mamba a Kwamitin Harkokin Kasashen Waje na Majalisar, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.
“Ina matukar damuwa kan tsarin Isra’ila kuma idan har burinta shi ne ta kawar da Hamas, to kisan da take yi wa fararen-hula, wanda ke zubar da kimarta, ya kamata a rage shi.”
Hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa ta sama da kasa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 10,600, galibinsu fararen-hula, a cewar Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza.
Source: TRTAFRICA