Gwamnatin Najeriya ta tsawaita dokar hana baki daga kasashen Brazil da India da Turkiya shiga cikin kasar ta saboda dakile yaduwar cutar korona wadda tayi kamari a cikin kasashen su.
Gwamnatin kasar ta kuma sanya sunan Afirka ta Kudu cikin jerin kasashen dake nahiyar Afirka da dokar ta shafa bayan kasashen Zambia da Rwanda da Namibia da kuma Uganda.
Shugaban kwamitin yaki da cutar kuma Sakataren Gwamnati Boss Gida Mustapha ya sanar da sabon matakin inda ya kara da cewar sabuwar dokar za tayi aiki na makwanni 4 kafin sake nazari akan ta.
Mustapha yace suna sanya ido akan abubuwan dake faruwa a kasashen duniya dangane da abinda ya shafi cutar domin daukar matakan da suka dace na kare lafiyar Yan Najeriya.
Sakataren Gwamnatin ya baiwa Yan Najeriya shawarar ci gaba da sanya ido sosai da daukar matakan kare lafiyar su ganin yadda ake samun sake dawowar cutar a wasu kasashen Afirka.
Shugaban kwamitin ya kuma bayyana cewar suna mayar da hankali akan batun samar da maganin rigakafi wajen ganin an yiwa jama’ar kasar allurar domin kare kan su daga harbuwa da cutar.
Gwamnatin ta najeriya na daukan wadannan matakan ne a dai dai lokacin da annobar cutar korona ke cin karen ta babu babbaka a manyan kasashen yammacin turai irin su amurka, ingila,italiya da sauran sa.
Ana sa ran gwamnatin ta najeriya ta samu karbar wasu karin allurar rigakafi kyauta domin cigaba da yakar yaduwar cutar ta korona mai hadarin gaske.
Wata matsala ta daban da ta addabi al’ummar najeriya bayan matsalar annaobar cutar korona itace matsalar tsaro, wacce zuwa yanzu tsaron kasar musamman arewacin kasar inda musulmi suka fi yawa kuma kungiyoyin ta;addanci na wahabiyawa suka mamaye manyan garuruwa.
An dai tabbatar da cewa tasirin kungiyoyin wahabiyanci yana taba babbar rawa wajen yaduwar rasahin tsaro a arewacin najeriya, matsalar da take bukatar lura ta musamman.