Firaiministar Finland da ke son kashe aurenta.
Firaiministar ƙasar Finland wadda ke shirin sauka daga mulki, Sanna Marin da mijinta, Markus Raikkonen sun shigar da kara a kotu domin raba aurensu.
Firaminista Marin ta rubuta a shafinta na instagram tana cewa “Mun gode wa Allah mun kwashe shekara 19 a tare har mun samu ƴa ɗaya.”
Marin za ta sauka daga muƙaminta bayan da jam’iyyarta ta faɗi zaɓe a watan jiya.
A bayanin da ta wallafa, Marin ta ce ita da mijin nata za su ci gaba da kasancewa abokai.
“Za mu ci gaba da haɗuwa a matsayin iyali.” In ji ta.
Ms Marin ta zama firaiminista mafi ƙanƙantar shekaru a lokacin da ta hau mulki a shekara ta 2019, lokacin tana da shekara 37.
Sai dai ta riƙa shan suka saboda yawan son masha’a, musamman a bara, lokacin da wani bidiyonta ya yaɗu a shafukan sada zumunta a wurin casu tana riƙe da wani kofi tana shaye-shaye, tana tiƙar rawa.
Wasu sun koka kan cewa lamarin ya zubar da kimar ƙasar ta Finland.
A lokacin, Ms Marin ta ce an ɗauki bidiyon ne a cikin gida lokacin da ta haɗa casu da ƙawayenta.
Sai dai ta yi gwajin barasa, wanda ya nuna cewa ba ta sha wani abu mai bugarwa ba.
A saboda haka wasu mata a ƙasar ta Finland suka riƙa wallafa bidiyonsu suna rawa a shafukan sada zumunta domin nuna goyon baya gare ta.
A yanzu dai gwamnatinta ta yi murabus bayan faɗuwa zaɓe, amma za ta ci gaba da kasancewa a muƙaminta har sai an ƙaddamar da sabuwar gwamnati.
Jam’iyyarta ta riƙa samun ƙuri’u masu yawa a zaɓukan da aka yi lokacin da take kan mulki saboda ƙoƙarin da ta yi na shigar da ƙasar cikin ƙungiyar NATO da kuma matakan da ta ɗauka na sawwaƙa wa ƙasar wahala sanadiyyar cutar korona.