Yadda uwargida za ta magance Amosanin kai wato (Dandruff) a saukake wanda yanzu yake addabar mata.
Abubuwa mafi saukin samu:
Abubuwan da za ki bukata su ne : Tumatir, Sabulun Salo, dan kwano ko roba, sai kuma Leda.
Uwargida ga yadda za ki hada:
Da farko dai za ki samu sabulun salonki kamar rabin gwangwanin madara amma ya danganta da yawan gashinki, ki samu tumatur masu kyau wanda suka nuna kamar guda uku idan manya ne ko hudu haka sun isheki.
Ki zuba sabulun salonki a cikin dan kwano ko roba sannan ki matse iya ruwan tumatur din ban da bayansa, sai ki jujjuya su sosai su hadu sannan ki bashi lokaci domin ya juku so sai za ki iya jika shi da safe idan da daddare za ki yi ki kwana da shi don an fiso ya dauki lokaci sosai a kanki.
Idan kuma ba ki samu ya kwana ba za ki iya amfani da shi duk lokacin da kika samu, kafin ki fara dama kin tsefe kanki kin taje shi so sai, sai ki raba gashinki kamar kashi hudu amma ba haka za ki bar shi ba za ki daure can saman gashin ban da kasansa yadda idan kin saka wannan hadin zai shiga kasan kanki sosai.
Sannan ki dauko wannan hadin tumatir da sabulun salon ki rika diiba a hankali kina zuba shi a kanki kina mummurza shi sosai domin ya shiga ko ina a cikin kanki musamman kasan gashinki, haka za ki yi ta yi har sai kin tabbatar wannan kaso hudun da kika yi wa gashinki duka sun jiku da wannan hadin, amma ki kula sosai ta yadda ba za ki bata jikinki ba ya zama iya kanki kadai kika shafa wannan hadin, bayan kin gama za ki samu leda mai kyau babba wacce za ta rufe miki kai ta yadda ko iska ba za ta shiga ba, idan kuma kina da shawercap sai ki sa ki dora hularki a kai, saiki bar shi ya yi kamar awa hudu ko biyar idan kuma na daren kika yi wanda shi ne ya fi to, gari na wayewa sai ki samu ruwan dumi ba mai zafi ba sai ki dauko sauran hadin ki yi amfani da shi wajan wankewa ki murza kanki sosai har sai kin ga ya fitar da kumfa, wajen wankin ki tabbatar duk ‘ya’yan tumatir din sun fita yayin da kike wankewa.
Shikenan sai ki taje shi sosai ki busar da shi tun da zamani ne yanzu uwargida za ki iya amfani da hand dryer wajan busarwa shikenan sai a shafe kai da man gashi. Uwargida wannan ita ce hanya mafi sauki da za ki yi maganin Amosanin Kai.