A tsakiyar Nijeriya, ana fuskantar wata cutar mai kisa ba tare da bata lokaci ba, cutar kuwa ita ce, cutar mashako, wadda ke bazuwa kamar wutar daji a wasu jihohin Arewacin Nijeriya da suka hada da Borno, Bauchi da kuma Kano.
Tuni kungiyar nan ta Likitoci ta ‘Médecins Sans Frontières (MSF)’ ta ankarar da al’umma tare da bayar da rahoton cewa, dubban yara sun mutu daruruwa ta kuma rasa rayukansu sakamakon cutar.
A ra’ayinmu, wannan babbar matsala ce da ke bukatar a gaggauta daukar matakin kawo karshen cutar a matakin kasa da ma duniya baki daya.
Da farko, mun yi tunanin cewa, cutar Mashako, wata cuta ce da aka manta da ita, aka barta a kundin tarihi da ke littatafai, godiya ga shirin rigakafi da aka yi a fadin duniya a shekarun baya. Amma kuma bayyanar ta a ‘yan shekarun nan ya nuna mana bukatar a kara daukar mataki na kariya ga al’ummar mu.
Tawagar Likitocin kungiyar MSF ta bayyana cewa, sun tabbatar da yi wa mutum 6,700 maganin cutar, a yayin da aka tabbatar da barkewar cutar a Kano, an kuma samu bullar cutar har sau 110 a Jihar Borno, a Jihar Bauchi kuma an samu mutum 21 da suka kamu ana kuma ci gaba da sa ido a kan sassan Nijeriya don kare yaduwarta.
Muna kira ga gwamnatoci da al’ummar duniya da kuma dukkan masu ruwa da tsaki da su hada hannu don kawar da cutar Mashako a Nijeriya, martaninmu mu shi ne zai tabbatar da kariya ga dubban ‘yan Nijeriya a cikin gida dama kasashen waje.
Wannan kuma ya kamata ya zama wani abin da zai farkar da Nijeriya da sauran kasashen duniya na bukatar su karfafa cibiyoyin kiwon lafiyansu, karfafa tsarin rigakafinsu da kuma kara zuba jari wajen samar da asibitoci da cibiyoyin lafiya a yankunan karkara da kuma samar da su a kusa da al’umma don inganta lafiyar al’umma gaba daya.
Camfe-camfe a kan maganin rigakafi yana daga cikin manyan matsalolin da yaki da cutar Mashako ke fuskanta, a kan haka dole a kara kaimi wajen fadakar da al’umma tare da nuna musu cewa, wannan abu ne da ya shafi lafiyarsu dana ‘ya’yansu. Ya kuma kamata a hada da ta shugabannin al’umma kamar masu unguwanni, sarakuna da sauransu.
Abin da ya kamata mu fahimta a nan shi ne, yadda aka samu barkewar cutar mashako a Nijeriya yana nuna mana cewa, wasu cututtuka masu yaduwa da aka manta da su suna iya sake bullowa idan kuma yi sakaci. Dole al’umma duniya su hada hannun don kawo dauki tare da maganin cutar Mashako a kasar nan, wannan lokaci ne na daukar mataki ba sai anjima ba musamman ganin abu ne da ya shafi rayuwar al’ummar duniya baki daya.
Source LEADERSHIPHAUSA