Cutar Kyandar Biri Ta Yi Kisan Farko A Turai.
Cutar kyandar biri ta yi kisan farko a wajen nahiyar Afrika.
Bayanai sun ce an samu mutum biyu da cutar ta yi ajalinsu a kasashen Spain da kuma Brazil.
Hakan ya sanya adadin mutanen da cutar ta kashe tun bayan bullarta a watan Mayu zuwa guda bakai, bayan biyar da ta kashe a Afrika inda aka gano ta gad an adam cikin 1970.
Spain ita ce wata kasa a duniya da aka fi samun yawan masu kamuwa da cutar inda take da mutum 4,298.
A ranar 24 ga watan nan ne hukumar lafiya ta duniya ta ayyana cutar ta kyandar biri a matsayin barazana ga sha’anin kiwon lafiya, domin karfafa matakan yaki da ita.
READ MORE : Karon Farko, Blinken Da Lavrov, Sun Tattauna Tun Bayan Rikicin Ukraine.
Mutum sama da 18,000 ne suka kamu da cutar a cikin kashe 78 na duniya a cewar WHO, kuma mafi yawan wadanda suka kamu da ita maza ne masu neman ‘yan uwansu maza.
READ MORE : Lavrov; Kasashen Yammacin Duniya Na Adawa Da Ci Gaban Afirka.
READ MORE : Kungiyar Hamas Ta yi wasti Da Ikirarin Isra’ila Na Kasancewar Makamai A Yankunan Farar Hula A Gaza.