Hukumar NCDC ta bayyana cewa cutar Kwalara ta fi kisan mutane fiye da cutar korona musamman a shekarar 2021.
Shugaban hukumar Ifedayo Adetifa ya fadi haka ranar Laraba a hira da yayi da tashar ‘Channels’.
Ya ce zuwa yanzu mutum 3,600 ne suka mutu a dalilin kamuwa da Kwalara a tsakanin watanni 11 da suka wuce.
Sannan a shekarar 2020 mutum 2,977 ne suka mutu a dalilin kamuwa da Kwalara.
Adetifa ya ce a yanzu haka hukumar ta aika da ma’aikatan ta zuwa duka jihohin da Kwalara ta barke domin dakile yaduwar cutar.
Ya ce cutar ta barke a dalilin rashin samun tsaftacen ruwa da Hana yin baya a waje da wasu jihohin kasar nan ke fama da su.
Adetifa ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka ta Samar wa mutane tsaftace ruwan sha da muhalli domin kare mutane daga kamuwa da Kwalara.
Korona
Daga ranar 21 ga Nuwamba 2021 mutum 3,566 ne suka mutu daga cikin mutum 103,589 da ake zargin sun kamu da cutar a jihohi 36 da Abuja.
NCDC ta ce jihohin Kano, Jigawa, Bauchi da Zamfara na cikin jihohin da suka fi yawan mutanen da suka kamu da cutar.
Hukumar ta ce korona ta yi ajalin mutum 2,977 sannan mutum 214,218 sun kamu da cutar daga shekaran 2020 zuwa ranar 1 ga Disemba 2021.