Wata mazauniyar birnin Lusaka Astridah Nkalamu ta haifi ɗanta na biyu a cikin shekarun 2000. Chota Kunda ya zame musu sanyin idaniya kamar dai yadda sauran jarirai suke, kuma wata ukun farko sun zama masu matuƙar daɗi ga uwar da ɗanta.
Kwatsam sai ya kamu da cutar sanƙarau. Yaron ya sha matuƙar wahala inda a ƙrshe cutar ta kurmantar da shi.
Tun daga nan rayuwarsu ta sauya gaba ɗaya.
“Kula da yaro mai lalurar nakasa wata rayuwa ce da ba za ka so yin ta ba, amma kuma ƙaddara ce da ba za a iya guje mata ba,” Astrida ta shaida wa TRT Afrika.
Fafutukar rayuwa
Uwar, ta shafe shekaru tana cikin matsanancin yanayi, amma duk da haka ɗan ƙaramin ɗan nata ba ya iya tafiya ko zama da kansa. Zuwa asibitin Chingwele da a yanzu ya koma Asibitin Matero ya zame musu jiki.
Amma maimakon yawan zuwa asibitin ya jigatar da jikin Astrida da ƙwaƙwalwarta, sai suka zama sanadin da ta samu ƙarfi da ƙarin gwiwar ci gaba da tafiyar da rayuwarta tsawon shekara 23.
“Ina cikin iyayen da suke kai ƴaƴnsu wajen gashi,” ta bayyana.
Tambayar da take yawan damun dukkansu ita ce: “Mece ce mafita ga iyayen da suke da ƴaƴa masu matsalar ƙwaƙwalwa da kuma nakasa?”
Abubuwan da irin wadannan yaran ke buata na da yawa: magani, abinci mai gina jiki na musamman, da kuma na’urorin za su taimaka musu.
Kafuwar babban shiri
A 2001, iyaye da dama sun fara tafiya ta hadin kai don samun ‘yancin kan sarrafa kudade. “Mun yi tunanin cewa a madadin mu shiga hatsarin cin bashi mai ruwa a yawa daga bankuna, me ya za ba za mu bude namu bankin a kauyenmu ba?” in ji Astrida.
Tunani ne mai sosa rai amma kuma mai ‘yantar da iyaye mata da mafi yawan su ke fama da da ciwukan kwakwlawa da ruhi — wasun sun rasa auren su, hakan ya sanya su fadawa matsalar rashin kudi.
Astrida ta shaida wa TRT Afirka cewa “Dole ne iyalin da ke da yaro nakasasshe su yi yaki da nuna bambanci. A wasu lokutan matsalar kyara na iya zuwa daga cikin iyalinka.”
Kungiyar iyaye da ke da yara masu bukata ta musaman ta Astridah Nkalamu
Babban abun da ya fi damun gidaje shi ne zamantakew da mijinta, wanda yake bukatar wayar da kai a wajen taruka. “A sannan ne na gan shi yana rungumar gaskiya,” in ji ta.
Yunkuri da martani
Sauki da Chota yake samu a hankali ya saukaka ayyukan Astrida da ma matsalolin da take fuskanta. A lokacin da yake shekara hudu, ya fara tafiya. Rayuwa ta fara dadi a yayin da wata sabuwar kaddarar ta sake zuwa; mijin Astrida ya rasu a lokacin da take da cikin dansu na hudu. A wajen ta, sake komawa ga matakin wahala na farko ne.
Ba da ban kauyen ba “kungiyar ajiya a banki”, to da Astrida ba ta samu yadda za ta kula da iyalinta ba.
A yanzu tana alfahari yayin waywaye ga shekarun baya d ayadda ta bunkasa, ta fadada gidanta zuwa mai dakuna uku.
Dan ta na fari ya karanta aikin jarida. Chota, duk da kurma ne na samun horo don zama malamin lissafi da yaren kurame. Na uku kuma na yi karatun digiri a f
annin sufuri da dakon kaya, inda dan autan kuma yake makarantar sakandire.