Annobar korona zata tsananta kamar yadda hukumumar lafiya ta duniya ta yi gargadi a jiya Juma’a cewa annobar Korona za ta yi tsanani a shekararta ta 2, a yayin da Japan ta fadada dokar ta baci a tsakankanin kiran da ake cewa a soke gasar Olympic.
Lamarin ya tsananta a Japan inda hukumomi suka fadada dokar ta-baci da suka sanya a dalilin annobar zuwa yankuna 3, makonni 10 kafin fara gasar wasannin motsa jiki ta Olympic, a yayin da masu adawa da gudanar da gasar suka mika wasika neman soke ta maai dauke da sa hannun sama da mutane dubu 300 da 50.
A yayin da Tokyo da sauran Yankuna ke karkashin dokar ta-baci har zuwa karshen watan Mayu, Hiroshima, Okayama da arewacin Hokkaido, inda za a gudanar da wasannin tsere za su bi sahu.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya ce gwamnatin kasar za ta fara yi wa jama’ar ta allurar rigakafin Corona, ba kakkautawa a dai-dai lokacin da cutar ke kara bazuwa a sassan kasar, ta yadda za a sauya jadawalin rigakafin ba dare-ba-rana don dakile yaduwarta.
A wani labarin na daban shugaba Macron ya ce abin fargaba ne yadda annobar cutar corona ke kara mamayar jama’a, wanda yanzu asibitoci a birnin Paris sun cika makil da marasa lafiya a cewar shugaban.
Macron ya ce za a fara wannan aikin rigakafin na annobar korona ba dare ba rana a ranar 1 ga watan Afrilu, kuma babu wasu ranaku da za a tsallake a aikin.
Kasar Faransa dai a yanzu na kokawa ne da cutar da ta sake barkewa a karo na uku, kuma tana cikin kasashen da ke fama da karuwar sabbin masu kamuwa da cutar a kullu yaumun.
Ya zuwa yanzu dai kasar na da alluran rigakafin cutar sama da miliyan 11 sai dai duk da hakan cutar na ci gaba da yaduwa kamar wutar daji a sassan kasar.
Ministan Lafiya na Faransar Olivier Veran ya ce rundunar sojin kasar za ta samar da manyan cibiyoyin bayar da alluran rigakafin guda 35 a fadin kasar, don saukaka aikin da kuma gaggauta yiwa jama’a.
Kawo yanzu dai kasar ta Faransa ta dogara ne da asibitocin cikin unguwanni da dakunan shan magani da na tiyata a matsayin wajen killace masu fama da cutar, a yayin da sauran kasashen turai ke amfani da filayyen wasanni.