Adadin Fiye da mutane miliyan 5 ne a nahiyar Afirka suka kamu da cutar Covid-19 tun bayan bullarta a watan Disambar 2019 a kasar China.
Afirka ce Nahiyar da cutar bata yi mata illa ba sosai, ta yawan adadin masu kamawu da ita da ma wadanda ta kashe, bayan ga Oceania.
Alkaluman hukumomin lafiyar kasashe da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tattara sun nuna cewa, mutane miliyan 5,008,656 suka harbu da cutar cikin kasashe da yankunan Afirka 54, kusan mutane 109,800 sun harbu ne cikin kwanaki bakwai da suka gabata, yayin da ta kashe sama da mutane dubu 134.
Bullar korona karo na uku
Yanzu haka wasu kasahen Nahiyar na fusknatar barazar barkewar cutar a karo na uku, inda ake kallon kasashen Masar da Afirka ta Kudu a matsayin kasashen da ke fama da bullar cutar a karo na uku, sai kuma Tunusia da Uganda da kuma Zambia da cutar ke kara tsanata.
A wani labarin nadaban hukumar lafiya ta duniya ta ce akwai yiwuwar kusan kashi 90 a kasashen Afrika za su gaza kan wa’adin yiwa al’ummominsu allurar rigakafin cutar Korona kafin watan Satumba, muddin basu gaggauta karbar sunkin alluran fiye da miliyan 200 ba.
A wani jawabi ta kafar intanet, daraktar sashin Afrika na hukumar lafiyar ta duniya Matshidiso Moeti, ta ce kasashe 7 cikin 54 na nahiyar ne ake kyautata zaton za su kai gaci a game da shirin yiwa al’ummominsu alluran rigakafin kafin cikar wa’adin da aka shata.
Adadin Akalla allurai miliyan 225 ne ake bukata cikin gaggawa idan har ana so akasarin kasashen su kai labari, kamar yadda kwararru suka tabbatar.
Adadin Kididdiga dai ta nuna kasa da kashi daya na alluran rigakafin Covid-19 sama da biliyan daya da miliyan 100 da aka rarraba a fadin duniya, nahiyar Afrika ta karba, a cewar hukumar lafiyar ta duniya.
Hakan yasa hukumar lafiyar ta bukaci kasashe masu hannu da shuni su taimaka wa kasashen da ba su da galihu domin samun daidaito wajen rabon alluran.