Gwamnatin kasar Amurka ta sake nanata bukatarta ta magana gaba da gaba da kasar Iran dangane da dage mata takunkuman tattalin arziki da kuma wasu al-amura.
An koma kan taburin tattaunawa dangane da daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar da kuma maido da ita Amurkan cikin yarjejeniyar JCPOA zagaye na 8 ne a cikin watan Dicemban da ya gabata, amma saboda janyewarta daga yarjejeniyar an ware Amurka a tattaunawar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka Ned Price yana sake nanata bukatar tattaunawa da kasar Iran gaba da gaba a kan batutuwan dauke mata takunkumai da kuma wasu al-amura a jiya Litinin.
Price ya bayyana haka ne bayan da ministan harkokin wajen kasar Iran Hosain Amir Abdullahiyan ya bayyana cewa Amurka ta bukaci magana gaba da gaba da Iran kan cire mata takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata sau da dama. Amma ministan ya ce, ba zai kore yiyuwar hakan ba, amma dole ne ganawar ta kasashen karkashin tattaunawar Vienna.
“Idan tattaunawar ta kaiga yamakata a yi magana da Amurka gaba da gaba, zamu shawarta don ganin yiyuwar hakan” inji Abdullahiyan..