Labaran da suke fitowa daga kasar Iraki sun nuna cewa an kaiwa wata tawagar sojojin Amurka hari a yankin Kadisiyya na lardin Kirkuk daga arewacin kasar.Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya kara da cewa a jiya ma an kaiwa wata tawagar sojojin Amurkan hari a tsakanin yankin Yusufiyya da Mahmodiyya da ke arewacin birnin Bagadaza.
Kafin haka dai kungiyoyi masu gwagwarmaya da ‘yan ta’adda a kasar ta Iraki sun sha alwashin sai sun kori sojojin Amurka daga kasar. Kuma sun kara da cewa zasu ci gaba da kai mata hare-hare har zuwa lokacinda zata kawo karshen samuwar sojojinta a kasar.