Ƴan ƙungiyar Taliban sun yi gumurzu da masu gadin iyakar Iran.
Kungiyar Taliban da ke mulkin Afganistan sun fafata da masu gadin kan iyakar Iran a kan iyakar ƙasashen biyu.
Mayakan sun ce an kashe daya daga cikinsu a fadan da aka yi a ranar Lahadi a kan iyakar da ke tsakanin lardin Nimroz na Afghanistan da Hirmand na Iran.
Kowace ƙasa ta ɗora wa ɗayar laifi akan lamarin, wanda shi ne fada na baya-bayan nan da aka yi tun bayan da kungiyar Taliban ta ƙwace iko da Afghanistan shekara daya da ta wuce.
A watan da ya gabata, Iran ta ba da rahoton mutuwar daya daga cikin masu gadinta a wani lamari da ya faru a wannan yanki.
Ba a san hakikanin yanayin fadan na baya-bayan nan ba, amma wani rahoton Iran ya ce an fara harbe-harbe ne a lokacin da kungiyar Taliban suka yi kokarin ɗaga tutarsu a yankunan da ba na Afghanistan ba.
READ MORE : Tunisia; An Gayyaci Jakadan Amurka A Ma’aikatar Harkokin Waje Kan Katsalandan Da Kasar Ke Yi.
Rahotanni sun ce ba a samu asarar rayuka ba a bangaren Iran.
READ MORE : Iran; Adadin Mutanen Da Suka rasa Rayukansu Sakamakon Ambaliyar Ruwa Yana Karuwa.