Ƙasashen duniya na Allah-wadai da Isra’ila bayan ‘yan sanda sun tarwatsa jana’iza.
Kasashen duniya na ci gaba da yin kakkausar suka kan abin da ‘yan sandan Isra’ila suka yi a wurin jana’izar ‘yar jaridar nan ta Al Jazeera, Shireen Abu Akleh.
‘Yan sanda sun dinga harbi da dukan masu jana’iza, ciki har da masu dauke da gawarta, lamarin da ya sa gawar ta kusa faɗuwa ƙasa.
Fadar mulkin Amurka ta White House ta nuna rashin jin dadinta kan abin da ya faru.
Mai magana da yawun fadar, Jen Psaki, ta ce: “Duk mun ga wadannan hotuna, suna da matukar tayar da hankali, abu ne da ya kamata a ce ya gudana cikin lumana.”
Kungiyar Tarayyar Turai ta EU ta ce ta yi “matukar kaɗuwa” da matakin na ‘yan sandan Isra’ila, wanda ta bayyana a matsayin “rashin mutuntawa”.
READ MORE : Siyasar Kano; Ganduje ya je kamun ƙafa gidan Shekarau.
An kashe ƙwararriyar ‘yar jaridar ta Aljazeera ne Abu Akleh yayin wani samame da Isra’ila ta kai gaɓar yammacin Kogin Jordan a ranar Laraba, wanda ta mamaye.
READ MORE : Daga Khashoggi zuwa Shereen Abu Akleh, Kisan ‘Yan Jarida ta Gwamnatin Danniya.
READ MORE : Martanin wasu kasashen Africa game da kisan da Isra’ila ta yi wa dan jaridar Al-Jazeera.