Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun ya ce, kasarsa za ta ci gaba da taka rawar gani, a fannin ingiza bunkasar nahiyar Afirka cikin lumana, tare da fadada hadin gwiwar nahiyar da sauran sassan kasa da kasa.
Zhang, wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, ya kuma yi amfani da zaman taron kwamitin tsaron MDD da ya gudana a ranar, mai taken “Hadin gwiwa tsakanin MDD da kungiyar AU” wajen bayyana cewa, a shekarun baya bayan nan, kungiyar AU da sauran hukumomin yankin Afirka, na aiki tukuru wajen tunkarar kalubalen zaman lafiya da tsaro, suna kuma kokarin ingiza matakan warware matsalolin nahiyar.
Ya ce yayin da ake tunkarar kalubale daban daban a sassan duniya da yankuna, kamata ya yi kwamitin tsaron MDD ya ci gaba da tallafawa AU, wajen karfafa wannan yunkuri. Kaza lika ya dace tawagogin wanzar da zaman lafiya na MDD su rungumi dabarun da AU ke amfani da su, kana su amince da sauye-sauyen yanayin da ake ciki, su kuma sauke nauyin dake wuyan su yadda ya kamata.
Zhang Jun ya kara da cewa, a halin da ake ciki, yankin kahon Afirka na fuskantar manyan matsaloli masu sarkakiyar warwarewa, kana ana fama da yanayin rashin tabbas a siyasar kasashen yammacin Afirka da Sahel, ga kuma kalubalen ’yan ta’adda dake haifar da tashin hankula, a babban yankin tafkin Chadi. Ya ce wadannan batutuwa ne masu matukar haifar da damuwa.
Don haka ya dace MDD ta tallafawa nahiyar Afirka, wajen cimma nasarar muradun dake kunshe cikin ajandar wanzar da ci gaba mai dorewa ta nan da shekarar 2030, kana ta kara azama wajen tallafawa yaki da talauci, da tabbatar da samuwar isasshen abinci, da karfafa samar da muhimman ababen more rayuwa, da fadada samar da guraben ayyukan yi.
Daga nan sai Zhang Jun ya jaddada matsayar kasar Sin, ta mara baya ga sanin makamar aiki tsakanin kasashen nahiyar Afirka, a matsayin daya daga muhimman ginshikai na hadin gwiwa da nahiyar, baya ga burin da Sin din ke da shi na taimakawa nahiyar a fannin bunkasa masana’antu, da zamanantarwa, da wanzar da ci gaba. (Mai fassara: Saminu Alhassan).
Source LEADERSHIPHAUSA