Shugaban Ukraine Voloymyr Zelensky ya sha alwashin samun nasara duk kuwa da yada Rasha ke ci gaba da dirar mikiya a gabashin kasar, a daidai lokacin da majalisar dinkin duniya ke yin wani yunkurin ganin an fitar da miliyoyin tan tan na hatsi daga kasar don kauce wa matsalar yunwa a duniya.
Sama da kwana 100 kenan yau da shugaban Rasha Vldimir Putin ya umurci dakarun kasarsa su afka wa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabraikru, inda aka yi asarar dubban rayuka, miliyoyin mutane kuma suka tsere daga gidajensu.
Jajircewar mayakan Ukraine dai ta taka wa dakarun Rasha birki a kokarin da suke na kama babban birnin kasar, Kyiv, lamarin da ya sa suka mayar da hankalinsu ga kame gabashin kasar.
A wani sakon bidiyo, Zelensky ya caccaki dakarun Rasha, inda ya ce a farkon fara yakin ne suke da ban tsoro.
A wani labarin na daban shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum, ya jaddada kiransa ga mayakan kungiyoyi masu ikirarin jihadi da ke da burin tuba a yayin wata ziyarar da ya kai yankin kudu maso yammacin kasar, yana mai cewa kofa a bude take ga irin wadannan mayaka.
A gaban dimbim al’ummar Torodi, a kusa da kan iyakar kasar da Burkina Faso, shugaba Bazoum ya ce ya sha kira ga mayakan da ke ta’addanci da sunan jihadi da su bar rayuwa mara amfani da ba za ta tsinana musu komai ba.
Ya ce lallai idan suka yi watsi da ta’addanci, hukuma za ta karbe su zuwa cikin al’umma, ta kuma sama musu aikin yi don tabbatar da ci gabansu ta fannin tattalin arziki, yana mai bayyana fatan suna sauraronsa.
A karshen watan Fabrairu ne shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya sanar da cewa ya fara tattaunawa da ‘yan asalin kasarsa da ke cikin kungiyar IS a wani yunkuri na lalubo zaman lafiya.