Zelensky, Ya Sake Nanata Bukatar Ganawar Keke-da-Keke Da Putin.
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya sake nanata kiran da ya yi kwanan baya na neman ganawa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a kokarin kawo karshen yakin na Ukraine.
Zelensky, ya shaida wa taron manema labarai a Kiev babban birnin kasar cewa, ba ya tsoron ganawa da Putin idan har za ta kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine.
Shugaban na Ukraine ya kara da cewa ganawar ta zama wajibi domin kawo karshen wannan rikici, ta hanyar diplomasiyya.
Kalaman na Zelensky na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai ziyarci birnin Kiev a wannan Lahadin.
Kawo yanzu dai an shiga wata na uku da mamayar da Rasha ta soma yi wa Ukraine da sunan matakin soji na kakkabe kasar daga wadanda ta danganta da ‘yan nazi.
READ MORE : An Yi Jerin Gwanon Tir Da Isra’ila A Wasu Kasashen Duniya.
Haka zalika a mako mai zuwa ne aka sa ran babban sakataren MDD, Antonio Guteress, zai ziyarci kasashen Rasha da kuma Ukraine, inda zai gana da shugabanin kasashen da zumar cimma matsaya ta kawo karshen yakin.
READ MORE : Aljeriya; Tabbun Ya Ce Alakarsu Na Daram Da Kasar Rasha.