Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce aikin tura karin dakaru zuwa kasarsa da Rasha ke yi na nuni da dimbim asarar da ta yi a yayin samamen da ta kaddamar, yana mai bayyana ta a matsayin asara mafi girma da Rasha ta taba fuskanta a cikin gwamman shekaru.
A wani jawabi da ya gabatar ta kafar talabijin, Zelensky ya bukaci Rasha da ta mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta don a samu sukunin kwashe fararen hula a birnin Mariupol mai tashar jiragen ruwa da ta wa kawanya.
Rahotanni daga biranen Donestk da Kyiv na cewa Rasha na ci gaba da luguden wuta musamman ma a wuraren da ake aikin kwashe fararen hula, kamar yadda gwamnonin yankunan suka bayyana a mabanbantan sanarwai.
A wani labarin na daban Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce ya zuwa yanzu an kashe ‘yan kasar da suka hada da fararen hula da sojoji sama da 135, yayin da aka shiga rana ta biyu a yakin da Rasha ta kaddamar kansu.
Rasha ta kwace iko da sararin samaniyar Ukraine
Rahotanni dai sun ce, Rasha ta kwace iko da tsaron sararin samaniyar Ukraine, kamar yadda wani babban jami’in leken asiri na yammacin Turai da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar, a yayin da dubban dakarun Rashan ke cigaba da dannawa cikin makwafciyar tasu da zummar mamaye Kyiv babban birnin kasar.
A baya bayan nan ne kuma Anton Herashchenko, mai baiwa ministan harkokin cikin gidan Ukraine shawara ya ce dakarun kasar sun yi nasarar kakkabo wani jirgin yakin Rasha a birnin Kyiv, wanda ya fada kan wani ginin fararen hula mai hawa 9 da ya kama da wuta.
Tun da farko dai an jiyo kara amai karfin gaske ta fashe-fashe a Kyiv babban birnin kasar ta Ukraine, wadanda daga bisani Herashchenko ya ce karar makaman kariyar da aka yi amfani da su ne wajen kakkab jirgin yakin na Rasha.
Rasha ta lalata cibiyoyin sojin Ukraine sama da 70
Rasha dai ta sanar da lalata cibiyoyin sojin Ukraine sama da 70, yayin da ita kuma rundunar sojin Ukraine ta ce dakarunta sun kashe sojojin Rasha kusan 50 tare da lalata jiragen yakinsu 6.
An dai yi ittifakin cewar yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine shi mafi girma da muni da aka gani a nahiyar Turai tun bayan yakin duniya na 2, inda wata kasa ta afkawa wata.