Zaɓen Najeriya 2023: Yadda al’ummar Najeriya ke dakon sakamakon zaɓen shugaban ƙasa
Tun da asubahin ranar Asabar ne al’umma a faɗin ƙasar suka ringa fita rumfunan zaɓe suna shiga layuka domin zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisar tarayya.
Duk da cewa rahotanni daga sassan ƙasar sun nuna cewa an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali, to amma an samu tashe-tashen hankula a wasu yankunan, inda aka far wa masu kaɗa ƙuri’a da farfasa akwatunan zaɓen, a wasu wuraren ma an ƙwace na’urar tantance masu kaɗa ƙuri’a (BVAS).
Hakan ya sa an tsawaita lokacin zaɓe a wasu jihohin zuwa ranar Lahadi.
Shiga nan domin duba sakamakon zaɓen shugaban Najeriya
A yanzu al’umma na dakon sakamakon zaɓe.
“Gaskiya na ƙagara na ga sakamako, saboda ina so in ga cewa wanda na zaɓa ya ci, na ƙagara sosai” – in ji wata da ta kaɗa ƙuri’arta a jihar Katsina, da ke arewacin ƙasar.
Bayanai daga jihohi na cewa a yanzu mutane sun dogara ne da kafafen yaɗa labarai domin samun bayanai kan sakamakon zaɓen na 2023.
Sai dai tun a ranar zaɓen ne ake ta wallafa sakamakon na rumfunan zaɓe daban-daban a shafukan sada zumunta.
Sai dai babu kaofofi masu zamansu da suka tabbatar da sahihancin wadannnan sakamakon.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokawa kan yadda ake amfani da irin waɗannan shafuka wajen yaɗa labaran bogi da na ƙanzon-kurege.
Sai dai duk da haka irin waɗannan labarai na ci gaba da yaɗuwa kamar wutar-daji.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar ce dai ke da ikon bayyana sakamakon zaɓen a hukumance.
A mafi yawan lokuta an fi sanya ido kan sakamakon shugaban ƙasa, inda a wannan karo aka samu manyan ƴan takara huɗu da ake sa ran za su taka rawar gani.
Sai kuma kujerun sanatoci 109 waɗanda aka yi takara, da kuma na ƴan majalisar wakilai 360.
A bayanin da ya yi ranar Asabar, shugaban Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya ce za a fara tattarawa da sanar da sakamakon zaɓen ne a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 12:30 na rana.
Rahotanni dai na cewa an samu fitowar al’umma da dama domin kaɗa ƙuri’a.
INEC ta ce masu kaɗa ƙuri’a miliyan 87,209,007 ne suka karɓi katin zaɓensu.
Ƴan takarar shugabancin Najeriya da suka fi shahara
Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas ne da ke kudu maso yammaci.
Ya yi sanata na wani lokaci a farkon shekarun 1990, wannan ne karon farko da yake takarar shugaban ƙasa a jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC).
Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno ne ke yi masa mataimaki.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar yana wannan takarar ne a karo na shida.
Ya yi wa’adi biyu a matsayin mataimakin shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.
Gwamnan jihar Delta da ke yankin kudancin Najeriya Ifeanyi Okowa, shi ne ke yi masa mataimaki a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Rabiu Kwankwaso tsohon gwamnan jihar Kano ne. Ya yi gwamna har sau byu, ya yi sanata tsakanin 2015 da 2019.
A baya an naɗa shi, a matsayin ministan tsaro.
Wannan ne karo na uku da yake neman babban ofishin. Takararsa biyu da ya yi a baya duka faduwa ya yi a zaɓen fidda gwani.
Yana takara ne da mataimakinsa Odiri Idahosa a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).
Tsohon gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabas, Peter Obi shi ne dan takarar shugaban ƙasar jam’iyyar Labour Party (LP).
Wannan ne karo na biyu da yake takara. Karon farko shi ne ya yi wa Atiku Abubakar mataimaki a 2019 karkashin jam’iyyar PDP.
Datti-Baba Ahmad ne yake yi masa mataimaki a takarar.