Zazzabin Malaria Na Barazana Ga Rabin Al’ummar Duniya.
Yau 25 ga watan April, ita ce ranar da MDD, ta ware domin yaki da zazzabin cizon sauro ko malaria.
Rahoton da hukumar lafiya ta duniya ta fitar ya nuna cewa rabin al’ummar duniya na fuskantar barazanar zazzabin na Malaria.
Kuma a rahoton da ta fitar hukumar ta ce a shekarar 2020 mutum miliyan 241 ne suka kamu da zazzabin cizon sauro a fadin duniya kuma 627 000 zazzabin ya kashe a kasashe 85.
Sannan mafi akasarin wadanda lamarin ya shafa sun kasance ne a nahiyar Africa inda dubban yara suke mutuwa a ko wacce shekara.
A cewar hukumar ta WHO, karuwar cutar a cikin watanni 12 da suka gabata, ya faru ne sanadin hargitsin da aka samu mai nasaba da annobar cutar corona.
READ MORE : Sojojin Isra’ila Na Ci Gaba Da Tsananta Kai Hari kan Masu Ibada A Masallacin Quds.
Domin rage tasirin zazzabin, hukumar ta ce an samar da magunguna na riga kafi ga mata masu juna biyu da kuma jarirai dake rayuwa a wuraren dake da hadarin zazzabin dama kuma masu balaguro.
READ MORE : Zelensky, Ya Sake Nanata Bukatar Ganawar Keke-da-Keke Da Putin.
READ MORE : An Yi Jerin Gwanon Tir Da Isra’ila A Wasu Kasashen Duniya.