Hukumomin lafiya a Birtaniya sun ce mutum guda ya mutu sakamakon harbuwa da cutar zazzabin lassa, a yayin da suke sanar da mutane uku da cutar ta kama a karon farko tun bayan shekarar Mutumin ya mutu ne a asibitin Bedfordshire da ke birnin Landan.
Dukanin mutane 3 da suka harbu da wannan cuta ‘yan iyali guda ne a gabashin Ingila, kuma sun yi balaguro zuwa Afrika ta yamma a kwanan nan.
Lassa, zazzabin ne mai tsanani da ke dangi daya da Ebola da kwayar cutar Marburg, sai dai bai kai su hadari ba.
Wannan zazzabin ya samu sunansa ne daga arewacin Najeriya, a lokacin da aka fara gano shi a shekarar 1969.
A wani labarin na daban Bayanai daga cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya a sun nuna cewa akalla mutane 32 ne suka rasa rayukansu sakamakon zazzabin Lassa cikin makonni uku.
A shekarar 2019, cibiyar ta ce an samu bullar cutar guda 796, yayin da a shekarar 2020, an tabbatar da adadin mutane 1,165 da suka kamu da cutar a yayin da ake tsaka da annobar korona.
Jihohin da abin ya shafa sun hada da Edo, Ondo, Bauchi, Benue, Oyo, Taraba, Ebonyi, Kogi, Kaduna, Katsina, Ebonyi, Plateau, Cross River, Borno, Anambra, Bayelsa, Jigawa, Kebbi, Ogun, Kwara, Lagos, Delta, Gombe, Nasarawa, Rivers da Enugu sai kuma birnin tarayya Abuja.