A yau Asabar masu zanga zanga a birnin Paris suka bukaci Tarayyar Turai ta haramta kayayyakin da ke da nasaba da ci da gumin ‘yan tsirarrun al’ummar Uighur da ke yankin Xinhjiang na kasar China.
Masu fafutuka da suka taru a dandalin Palace de la Republic a birnin Paris a Asabar, sun bukaci Tarayyar Turai ta dau mataki a game da take hakkin bil adama da ake yi wa al’ummar Uighur a lardin Xinjiang na arewa maso yammacin China.
Zanga zangar na zuwa ne makonni bayan da shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta sanar da shirin haramta shigowa da kayayyakin da aka samar da su ta wajen aikin dole.
A wani labarin na daban a wata ganawa da tashar France24, Raphael Glucksman, dan majalisar Tarayyar Turai, ya zargi kamfanonin Turai da ke samun riba a kana bin da China ke yi da kokarin dakile matakin haramta kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin dole.
Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun amince da sanya takunkumi kan manyan jami’an gwamnatin China dangane da yadda kasar ke cin zarafi tare da kuntatawa tsirarun musulmi ‘yan kabilar Uighur.
A wani taron ministocin wajen kasashen 27 ranar Litinin mai zuwa ne takunkuman za su tabbata wadanda za su shafi hatta kasashen Rasha Korea ta Arewa da Eritrea da kuma Sudan ta Kudu baya ga Libya dukkaninsu saboda tuhume-tuhume ko kuma zargin take hakkin bil’adama.
Tuni dai China ta nuna bacin ranta game da yunkurin sanya mata takunkumai kan halin da ‘yan kabilar ta Uighur ke ciki a yankin Xinjiang inda jakadan kasar a EU Zhan Ming ke cewa Turai na shirin kakabawa Beijing takunkuman bisa kaffa hujja da kare-rayi baya ga rahotannin da basu da tushe.
A cewar Mr Zhan, China na bukatar tattaunawa ta fahimtar juna tsakaninta da EU amma kafin wannan yakamata Turai ta yi tunani sosai gabanin kakaba mata takunkuman wadanda za su shafi alakar da ke tsakaninsu, domin kuwa a acewarsa Beijing ba za ta zuba ido ba tare da daukar mataki ba.
Mr Zhan ya nanata cewa China ba ta da hannu a zargin da ake mata kuma a shirye ta ke ta mayar da martani kan duk wani yunkuri ko kuma barazana ga tsaro da manufofinta.