Zanga zangar da akayi a birnin paris ‘yan sanda sun yi amfani da feshin ruwa da kuma barkonon tsohuwa wajen tarwatsa daruruwan masu zanga-zangar Allah-wadai da hare-haren Isra’ila kan Falasdinawa a birnin Gaza.
Tun a makon jiye ne dai rundunar ‘yan sandan Faransa ta haramta gudanar da zanga-zanga haka zalika kotu ta tabbatar da haramcin, domin gudun barkewar irin tashin hankalin da aka gani yayin makamanciyar ta da ta gudana yayin yakin da aka gwabza tsakanin Isra’ila da Falasdinawa a shekarar 2014.
A waccan lokacin dai masu zanga-zanga din sun yi amfani da damar wajen afkawa mujami’un Yahudawa da wasu muradunsu a sassan kasar ta Faransa.
‘Yan adawa a Faransar dai sun caccaki matakin haramta gudanar da zanga zangar a bana, abinda suka bayyana a matssayin take yancin fadin albarkcin baki.
A wani labarin na daban an shiga rana 6 a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa kan Falasdinawa a zirin Gaza, inda a yau asabar barin wutar jiragen yakin Isra’ilar ya kai ga kashe mutane 10 cikinsu har da kananan yara 8 a wani sansanin ‘yan gudun hijira.
Farmakin Isra’ilar ya kuma rusa gine-ginen da suka kunshi ofisoshin kamfanin dillancin labarai na AP da kuma kafar talabijin ta Aljazeerah.
Kawo yanzu akalla Falasdinawa 140 suka mutu cikin har da yara kanana 39, yayin da wasu kimanin 950 suka jikkata, tun bayan kaddamar da hare-haren da Isra’ila tayi kan birnin Gaza a ranar litinin da ta gabata.
A gabar yamma da kogin Jordan kuwa rahotanni sun ce jami’an tsaron Isra’ila sun kashe Falasdinawa akalla 13, yayin arrangamar da suka yi da Falasdinawan dake zanga-zanga kan neman dakatar da hare-haren da aka kaddamar kan birnin Gaza.
A bangaren Isra’ila kuwa, ta ce akalla mutane 9 mayakan Hamas suka kashe mata, sakamakon daruruwan rokokin da suka harbawa kan wasu biranen ta daga Gaza.
Majalisar dinkin duniya ta kiyasata cewar Falasdinawa dubu 10 sun rasa muhallansu dalilin rikicin da ya barke a makon jiya, tare da bayyana fargabar tagayyar da fararen hular suka yi ka iya fin haka muni a nan gaba kadan.