Zanga-zangar dubun dubatan mutane daga Afirka ta Kudu, Amurka da New York na nuna goyon bayan Gaza, da gagarumin zanga-zangar adawa da Netanyahu a Tel Aviv, da bayanin taron kasashen musulmi a Riyadh, na daga cikin abubuwan da ke faruwa a Gaza.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Rasha Today cewa, ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Gaza da ake zalunta a fadin duniya.
A birnin Cape Town, babban birnin kasar Afirka ta Kudu, an gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu da dubun dubatar jama’a da kuma yin Allah wadai da hare-haren wuce gona da iri na gwamnatin sahyoniyawan.
Mahalarta wannan zanga-zangar sun rera taken nuna rashin amincewa da Amurka da kuma yadda take da hannu a kisan gillar da Isra’ila ke yi a yayin da suke rike da tutocin Falasdinawa da kwalaye da rubuce-rubucen nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu.
Titunan birnin New York na Amurka, da kuma babban birnin kasar Ingila, a yau, a rana ta 36 da guguwar Al-Aqsa, ta samu dimbin ‘yan kasar da ke goyon bayan Falasdinawa, wadanda suka bukaci tsagaita bude wuta a Gaza. .
A halin da ake ciki kuma a birnin Landan, ‘yan sandan Birtaniya sun rufe titunan da ke kan hanyar zuwa ofisoshin jakadancin Amurka da na Sahayoniya saboda fargabar hare-haren da masu zanga-zangar ke kaiwa.
Zanga-zangar nuna adawa da Netanyahu a Tel Aviv
Dubban mazauna yankunan da aka mamaye sun sake gudanar da zanga-zanga a birnin Tel Aviv a daren jiya Asabar, domin neman a sako fursunonin yahudawan sahyoniya da ke hannun kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa a Gaza.
Bukatar shugabannin kasashen musulmi na gaggauta kai agaji zuwa Gaza
Taron na musamman na shugabannin kasashen Larabawa da na Musulunci ya kawo karshen aikinsa tare da fitar da sanarwa dangane da wajabcin wargaza kewayen Gaza da isar kayan agajin jin kai.
A cikin wannan bayani, an jaddada bukatar cibiyoyi na kasa da kasa da su shiga yankin zirin Gaza tare da cikakkun tawagoginsu don tallafawa hukumar agaji ta MDD UNRWA.
Har ila yau taron na kasashen musulmi ya sanar da cewa, yana goyon bayan kasar Masar wajen tinkarar sakamakon wannan danyen aiki na wuce gona da iri kan Gaza na shigo da kayan agaji cikin gaggawa, wanda zai ci gaba babu yankewa.
Source: IQNAHAUSA