Kyaftin din tawagar kwallon kafar Masar Mohammed Salah ya sake jaddada kudirinsa na lashe gasar Afrika ta AFCON da ke gudana a kamaru.
Masar za ta gwabza da Morocco a wasan quarter finals, kuma salah ya kagara ya jagoranci kasarsa zuwa ga nasara bayan da ta sha kashi a wasan karshe a shekarar 2021 a hannun Kamaru.
Salah ya ce kofin AFCON ne abin da yake matukar bukatar ya lashe, duk da cewa ya lashe kofin firimiyar Ingila da na zakarun nahiyar Turai.
A wani labarin na daban Shugaban hukumar kwallon kafar Masar, Hani Abou Rida ya ajiye aikinsa jim kadan bayan da kasar ta fice daga gasar cin kofin kasashen Afirka a ranar asabar.
Daga shekarar 2016 Rida ya soma jagorantar hukumar kwallon Masar, kuma a karkashinsa ne kasarta ta fice daga gasar cin kofin duniya a zagayen farko na matakin rukuni.
Nasarar ta Afrika ta Kudu kan Masar ta kawo karshen sanya mai masaukin bakin da ake cikin kasashen da ake saran za su iya lashe gasar ta bana, wadda a baya Masar din ta lashe kofinta harsau bakwai.