Kasar Zambia ta ce ta shirya jan hankalin karin Sinawa masu zuba jari, idan ta halarci taron baje kolin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afrika karo na 3 dake karatowa.
Baje kolin karo na 3 mai taken “Ci gaba na bai daya, Makoma ta bai daya” zai gudana ne daga ranar 29 ga watan Yuni zuwa 2 ga watan Yuli a lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin. Baje kolin wanda aka fara gudanar da shi a shekarar 2019, katafaren dandali ne na karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afrika.
Ministan kula da kasuwanci da cinikayya da ma’asanantu na Zambia Chipoka Mulenga, ya bayyana cewa zai jagoranci tawagar ‘yan kasuwar kasarsa zuwa baje kolin, kuma kawo yanzu jimilar kamfanoni 21 sun bayyana sha’awar shiga tawagar. A cewarsa, ba za a bar su a baya ba, wajen cin gajiyar wannan dama da kasar Sin ta samarwa Afrika, da sauran kasashe.
Ministan ya kara da cewa, Zambia ta na matukar son sanin yadda Sin ta samu nasarori a fannin raya kasuwanci. (Fa’iza Mustapha).
A wani labarin na daban kungiyar Kwallon Kafa ta Inter Milan ta doke abokiyar hamayyarta AC Milan da ci daya mai ban haushi da ya ba ta damar zuwa wasan karshe na gasar zakarun turai.
Tun da fari dai a satin da ya wuce Inter Milan ta doke AC Milan da ci 2 har gida, lamarin da ya sanya ta karkare wasanni biyu da kwallaye uku.
Inter Milan ta isa wasan karshe na gasar bayan shafe shekara 13 ba tare da ta sake zuwa wannan mataki ba.
Dan wasan gaban kungiyar Lautaro Martinez ya jefa kwallon daya da ta raba gardamar wasan.
A daren yau kuma za a fafata tsakanin Manchester City da Real Madrid da misalin karfe 8 na dare agogon Nijeriya.
Duk kungiyar da ta yi nasara za ta fafata wasan karshe da Inter Milan.