Karo na hudu kenan da ake tunawa da zagayowar kisan kwamnadan Qudus na sojojin Iran Janaral Kasim Sulaimani.
Sulaimani wanda sojan Amurka suka kashe a wani harin kwanton bauna ranar juma’a 2 ga watana janairun shekarar 2020 a kusa da filin sauka da tashin jirage na Bagdad babban birnin kasar Iraqi.
Duk a cikin ayyukan tunawa da shahadar ta Kasim Sulaimani shugaban kasar Iran, Sayyid IbrahimR’esi ya gana da ‘ya’yan Sulaimani din kamar yadda hotuna suka bayyana dagane da faruwar hakan.
Idan wannan lokaci na tunawa da shahadar Kasim Sulaimani dai ya gabato Iraniyawa kan shiga yanayi mai ban sha’awa na shirya taruka, samar kirkirar wakoki gami da kide kide masu alaka da tunawa da ‘yan mazan jiya duk domin nuna kaunar su ga gwarazan su musamman dai Sulaimani.
Kasim Sulaimani dai na cikin ‘yan gaba gaba wajen taimakion falasdinawa, wanda hakan ne ma yasa Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran ya taba cewa ” Wannnan mutum ya taimaki falasdinawa”
Kamar yadda kafar sadarwa ta Mehr News ta wallafa a shafin ta na yanar gizo ta tabbatar da cewa duk a cikin ayyukan zagayowar Ranar Shahadar ta SA Iyalan Kasim Sulaimani sun gana da babban jagoran al’ummar Iran, Ayatullah Ali Khamenei a gidan sa dale babban birnin Tehran.
Tashar yada labarai ta Shavakeh 5 ma ta Bayyana cewa al’ummar Iran da yawa ne suke tururuwa zuwa garin su Sulaimani kuma inda aka binne shi domin nuna soyayyar su gare Shi.
Kuma an kirkire take da wakoki kala Kala masu dauke da salon tausayawa gami da soyayya ga babban gwarzon da al’ummar Iran keyi ma kallon babban abin alfahari.