Sama da masu kada kuri’a miliyan 112 a Rasha da yankuna hudu na Ukraine da ke karkashin ikon Rasha ne za su kada ƙuri’unsu cikin kwanaki uku – daga ranar Jumma’a – domin zaben shugaban kasar karo na takwas.
Masu kaɗa ƙuri’a za su kada kuri’unsu har zuwa ranar Lahadi domin zaban shugaban da zai jagorance kasar Rasha nan gaba tsakanin ‘yan takara hudu.
Ana hasashen shugaba Vladimir Putin zai sake lashe kujerar a karo na biyar.
Zai tsaya takarar ne a ƙashin kansa, tare da goyon bayan jam’iyyar United Russia mai mulki da kuma A Just Russia – For Truth.
Vladislav Davankov, mataimakin shugaban majalisar wakilar kasar Rasha, shi ne dan takarar jam’iyyar New People da aka kafa a shekarar 2020.
Sauran ƴan takara biyun da za a fafata da su sune Leonid Slutsky, shugaban jam’iyyar Liberal Democratic Party of Rasha, da ɗan takarar jam’iyyar gurguzu Nikolay Kharitonov, wanda ke jagorantar kwamitin majalisar dokokin Rasha kan raya yankunan Gabas mai Nisa da yankunan Arctic mai yawan kankara na kasar.
Zabe na kwanaki uku
Zaben shugaban kasa na 2024 a Rasha shi ne karo na farko da za a gudanar da zabe a kasar cikin kwanaki uku na baya-baya da aka gudanar an yi su ne cikin yini guda.
Ko da yake an yi amfani da tsarin kada kuri’a na tsawon wasu kwanaki gabanin zaben raba gardama na kundin tsarin mulkin Rasha a 2020.
A cewar hukumar zaɓe na Rasha, kimanin mutane miliyan 112.3 ne suka yi rajista don kada kuri’a a zaben.
Wannan adadin ya hada da mutane a yankuna hudu na Ukrainian da Rasha ta mamaye ba bisa ƙa’ida ba a ranar 30 ga Satumba, 2022 wato yankin – Donetsk da Kherson da Luhansk, da kuma Zaporizhzhia.
Kusan masu kada kuri’a na Rasha miliyan 1.9 za su kada kuri’arsu a ofisoshin jakadancin kasarsu da ke waje.
Yayin da aka fara zaben a hukumance a ranar Juma’a, tun daga ranar 25 ga watan Fabrairu wadanda ke zaune a yankuna masu nisa na Rasha, nesa da rumfunan zabe suka fara kada kuri’arsu.
DUBA NAN: Majalisar Amurka Zata Haramta Tiktok A Kasar
Sama da masu sa ido kan zaben 200 daga kasashe 36 da kungiyoyin kasashen wajen biyar ne za su halarci zaben.