Yan ƙasar Senegal na kaɗa ƙuri’a ranar Lahadi a zaɓen shugaban ƙasar bayan an shekaru uku ana tayar da jijiyoyin siyasa sakamakon tuhumar da aka yi wa jagoran ƴan hamayya Ousmane Sonko da kuma fargabar da aka yi cewa shugaban ƙasar zai tsawaita wa’adin mulkinsa a zaben Senegal din.
Ƴan takara 19 ne za su fafata domin neman wanda zai maye gurbin Shugaba Macky Sall, wanda zai sauka daga mulki bayan ya kammala wa’adi biyu.
Mutum miliyan 7.3 ne suka yi rajista a zaɓen sai dai ana ganin fafatawar za ta fi zafi tsakanin ɗan takarar gamayyar jam’iyyu masu mulki firaiminista Amadou Ba and da babban ɗan hamayya Bassirou Diomaye Faye.
Dukansu sun taɓa aiki a hukumar karɓar haraji ta ƙasar, sai dai yanzu kowannensu yana da manufofi da suka sha bamban da na ɗayan. Ba, mai shekara 62, ya yi alƙawarin ci gaba da tsarin da shugaba mai ci yake kai, yayin da Faye, mai shekara 43 ya sha alwashin kawo gagarumin sauyi.
Kowannensu ya bugi ƙirji cewa zai lashe zaɓen a zagayen farko — sai dai akwai yiwuwar ta tafi zagaye na biyu, domin kuwa akwai ƴan takara 15 a zaɓen, ciki har da mace guda ɗaya.
Za a rufe rumfunan zaɓe ne da misalin ƙarfe shida na yamma a agogon Dakar kuma ana sa ran soma sanar da sakamakon zaɓen da tsakar dare.
Sai dai ba za a sanar da takamaiman wanda ya lashe shi ba wataƙila sai mako mai zuwa.
Ana kallon Senegal a matsayin ƙasar da ke da zaman lafiya a harkokin siyasa, sai dai matakin da Shugaba Macky Sall ya ɗauka na ɗage zaben wanda ya kamata a gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu ya haddasa zanga-zangar da ta kai ga mutuwar mutum huɗu.
DUBA NAN: An Sako Daliban Kuriga Da Aka Sace A Jihar Kaduna
Ɗaruruwan masu jami’ai daga Tarayyar Afirka da ECOWAS da kuma Tarayyar Turai ne za su sanya ido kan zaɓen.