A yau ashirin da shidda ga watan mayu ne ake gudanar da zaben shugaban kasa a kasar siriya kuma an samu fitowar al’ummar kasar siriya daga sassa daban daban masu kishi da kuma son cigaban kasar ta siriya da suke tuttudo santocin jefa kuri’a domin kada kuri’ar su.
Wani abnin sha’awa da birgewa gwamnatin kasar mai ci karkashin jagorancin Bashar Al-Assad ta sanar da cewa hatta ‘yan kasar ta siriya wadanda suke kasashen ketare zasu samu damar kada kuri’un su domin an samar kyakykyawan yanayin hakan.
Wakilin ,u ya tabbatar mana da cewa a yanzu hakan dai jefa kuri’u yayi nisan gaske a cikin kasar ta siriya dama kasashen da siriyawan suke kuma ana sa ran a kammala zaben cikin nasara.
Shugaba Bashar Al-Assad dai yana cikin ‘yan takara uku da suka fito domin neman sahhalewar al’ummar kasar ta siriya a matsayin shugaban kasa a wannan karon kumamamwa.
Ana ganin dai a kwai alamun shugaba Bashar Al-Assad din ya lashe zaben duba da cewa yana da farin jini sosai da soan gaske a tsakanin siriyawan kuma bayan babban aikin da yayi na fatattakar ‘yan ta’adda daga kasar tare da taimakon Kasar Jamhuriyyar Musulunci Ta Iran da kuma Rasha.
Zaben na siriya ya gamu da suka daga kasashen yammacin turai wanda aka alakanta hakan da kokarin su na hana samar da tabbatacciyar gwam,nati wacce zata kawo wanzuwar zaman lafiya a kasar ta siriya da ta sha fama tashe tashen hankula daga ‘yan ta’addan ISIS.
An gano shugaba bashar al-assad a mazabar sa ta douma yana kada tasa kuri’ar kamar yadda kafar sadarwa mallakin Iran ta rawaito.
Fitowar al’ummar siriya dai bai yima kasashen yamma dadi ba domin hakan kamar ya karya musu gwuiwa da kuma shirin su na kara sanya kasar ta siriya cikin mummunan yanayi bayan kokarin da shugaba bashar al-assad yayi na ceto kasar ta siriya.