Yahudawan kasar Isra’ila za su dumfari rumfunan zabe a ranar Talata domin kada kuri’ar zaben shugaban kasa a inda Shugaba Benjamin Netanyahu ke kokarin ganin ya kai labari a siyasance.
Ga abubuwa biyar da yakamata a sani game da zaben da kuma abubuwan da ka iya biyo baya.
1. Wannan ne zaben da za a fafata kwaraibayan shekaru da dama
Benjamin Netanyahu na takarar shugabancin kasar karo na biyar.
Idan aka kara zabarsa, zai wuce wanda ake ganin ya kafa Isra’ila wato David Ben-Gurion a matsayin Firai Ministan da ya fi dadewa.
Amma duk da haka Mista Netanyahu na fuskantar zargin cin hanci, wanda ana jiran babban alkalin kasar ya yanke hukunci kan lamarin.
Akwai Mista Benny Gantz wanda shi ne babban abokin karawar Netanyahu wanda shi ne tsohon shugaban sojojin kasar.
Za a iya cewa Mista Gantz sabon shiga ne ga siyasa kuma zai iya karawa da Netanyahu wajen samar da tsaro wanda shi ne babbar matsalar da ake tattaunawa ta zabe a kasar.
2. Shugaban jam’iyyar da bai da kujeru da dama, ba lallai ya zama Firai Minista ba
Babu wata jam’iyya a Isra’ila da ta taba samun rinjaye a kujerun majalisar kasar, a ko da yaushe kasar tana samun hadakar jam’iyyu ne.
Wannan na nufin ba wai jam’iyyar firai minista ba ce a kullum take lashe zaben kasar, amma wanda ya yi kokarin hada kan jam’iyyun domin samun a kalla kujeru 61 cikin 120 a majalisar.
Wasu hasashe na nuna cewa Mista Netanyahu ya fi kokarin yin hadaka bisa ga Mista Gantz sakamakon kusancin da Netanyahu yake da shi da wasu masu ruwa da tsaki na sauran jam’iyyu da kuma malaman addini a kasar.
3. Rashin mayar da hankali kan samar da zaman lafiya da Falasdinawa
A makonnin da suka gabata, an ta samun fargaba tsakanin Yahudawan Isra’ila da kuma raunanan Falastinawa a Gaza kuma ana sa ran Shugaban Amurka Donald Trump zai bayyana shirinsa na kawo karshen doguwar rashin jituwar da ke tsakanin Isra’ila da Falasdinawa bayan zaben.
Amma hanyoyin da za a bi domin samar da zaman lafiyar ba su zamo ababen tattaunawa ba a lokacin muhawarar zaben.
Yahudawan Isra’ila ba su da yakinin cewa wannan jita-jitar da ake yi na samar da zaman lafiya tsakanin kasashen da gaske ne.
Wasu daga cikin jiga-jigan na hannun daman Netanyahu a halin yanzu daga bangaren ‘yan hadaka sun fito fili, sun nuna adawarsu kan batun kafa kasar Falasdin da kuma bama falasdinawa ‘yancin rayuwa kuma suna so su mallaki gabar yamma na kogin Jordan.
Taken kamfe din Netanyahu na alamar shudi da fari na alamta rabuwa da Falasdin, amma hakan bai ambaci cewa ko za su samu kasar su ta kansu ba.
Haka kuma, hakan na alamta hadin kan Jerusalem a matsayin babban birnin Isra’ila duk da wannan bangaren hakkin Falasdinawa ne.
Bangaren Mista Gantz sun bayyana cewa suna son ci gaba da iko da gabar yamma da kogin Jordan.
Jam’iyyar Labour ta Isra’ila wace ta kulla yarjejeniya da Isra’ila a shekarun 1990 ta rasa farin jini a wurin masu zabe.
4. Yawan mutane zai taka rawa a zaben
Akwai masu kada kuri’a miliyan 6.3 a kasar kuma addinai da al’adu da kuma akidun masu zaben za su taka muhimmiyar rawa a zaben.
Addinin Haredi na kasar na da milioyin mutane.
A al’adance, Yahudawa na asalin kasashen Turai na jin maganar malaman su kuma suna zabe kan jam’iyyun da suka amince da su.
Amma a yanzu akasari suna zaben jam’iyyar da ke hanyar daidai.
5. Wanda ake ganin bai da tasiri na iya zama mai fada aji
Shugaban jam’iyyar ‘yan kishin kasa ta Zehut Party wato Moshe Feiglin na iya zama wanda zai yi sanadiyyar kawo shugaba a kasar a tataunawar da za a yi nan gaba ta hadaka.
Mista Feiglin ya bayyana cewa bai da wani takamaiman zabi tsakanin Netanyahu da kuma Benny Gantz.
Yana da tsatsauran ra’ayi kan Falasdinawa kuma yana so ya kore su daga gabar kogin Jordan da kuma zirin Gaza.
Kuma yana kira ga a bude sabon wurin bauta na uku na Yahudawa a filin Jerusalem wanda aka fi sani da Temple Mount, Musulmi kuma na kiran wurin al-Sharif wanda a nan ne masallacin al-Aqsa yake.
Source:legithausang