A ranar juma’ar da ta gabata ne Iraniyawa sukayi dafifi domin zaben sabon shugaban kasa wanda ake sa ran zai gudanar da kasar zuwa shekaru hudu masu zuwa.
Zaben na jamhuriyar musulunci ta Iran ya biyo bayan rasuwar shugaba Ibrahim Ra’isi wanda ya rasu a wani hadarin jirgin sama da ya auku kwanaki arba’in da suka gabata.
Kundin tsarin mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran dai ya wajabtawa Gwamnatin rikon kwarya ta gudanar da zabe a kasa da kwanakin hamsin idan irin haka ta faru.
Gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin Muhammad Mukbeer ta gudanar da zaben kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya bukata, zaben da ‘yan takara hudu suka taka rawa.
Sai dai kundin tsarin mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran ya bukaci dan takara ya samu kaso hamsin da daya cikin dari na kuri’un da aka kada kafin ya zama shugaban kasa, sharadin da babu dan takarar da ya iya cikawa a zaben na ranar juma’a.
Hukumar zaben kasar ta sanar da gudanar da zango na biyu na zaben inda ‘yan takara biyu da suka rage zasu fafata ‘yan takarar sune Masood Pezeshkiyan wanda ke da ra’ayin bibiyar turawa da neman shiri da su kuma shine kasashen turawa suke so kuma suke tallatawa a kafafen yada labaran su.
Dan takara na biyu Sa’eed Jalili shine mai ra’ayin ‘yan mazan jiya wanda bashi da farin jini sosai a wajen masu kudi amma talakawa suna son sa sosai, yayi alkawarin taimakon talakawa kuma bazaiyi biyayya ga turawan yamma ba.
Jagoran kasar dai yayi kira ga Iraniyawa da su fito domin kada kuri’un su domin tabbatar da cigaban kasar.
DUBA NAN: Zafi Yayi Sanadin Mutuwar Fiye Da 900 A Hajjin Bana
Duk da matsanancin zafi da akeyi a kasar wanda yake hana fitowa da rana a wasu bangarorin kasar mutane sun fito zaben inda hakan ya wajabta kai zaben har sha biyun dare sakamakon fitowar mutane da dama bayan dare yayi.