Zaben 2023; Dattawan Arewa Suna Son A Zabi Atiku A Shekara Mai Zuwa.
‘Yan siyasa a arewacin Najeriya suna son a zabi Atika Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasa, a zaben shekara mai zuwa a matsayin shugaban kasa
Jaridar leadership ta Najeria ta nakalto tun bayan da Atiku ya lashe zaben fidda dan takara a jam’iyyar PDP a makon da ya gabata ne, wasu shuwagabannin arewa daga ciki har da Janar mohammad Aliyu Gusau mai ritaya suke ganin yakama ‘yan arewa su marawa Atiku baya, sannan ana saran Gusau zai gana da tsohon shugaban kasa Janar Babangida mai riya a yau Litinin don gabatar da Atiku gareshi.
Labarin ya kara da cewa Atiku ya kada gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike da kuma Bala Muhammad na jihar Bauchi, da Bukula Saraki tsohon shugaban majalisar dattawan kasar.
READ MORE : Iran; Hukumar IAEA Taki Bayyana Hadin Kan Da Iran Ta Bata A Rahotonta Na Baya-Bayan Nan.
Wata majiya ta fadawa jaridar Leadership kan cewa Babangida da Guasu sun bukaci dukkan yan takara a jam’iyyar PDP su janye su barwa Atiku tun kafin a gudanar da zaben fidda yan takarar, amma wasu suka ki.
READ MORE : Kasashen Turai Sun Debe Kauna Daga Sayen Mai Daga Rasha.