Za’a Dawo Da Tsarin Karba-karba Na Sojojin MDD A Mali, Bayan Wata Guda Na Dakatarwa.
Gwamnatin Mali, ta ce za’a dawo da tsarin karba karba da sojojin tawagar wanzar da zaman lafiya na MDD ke yi a kasar daga ranar Litini.
Za’a dawo da tsarin ne bisa sabon salo kamar yadda ministan harkokin wajen Mali ya sanar wa kamfanin dilancin labaren AFP.
Ita ma tawagar Minusma ta tabbatar da labarin, wanda ke zuwa wata guda bayan da gwamnatin Mali ta sanar da dakatar da tsarin.
A sabon tsarin, an ce daga yanzu tawagar ta Minusma ce zata kula da abunda ya shafi rundunonin da zasu shiga Malin, sannan ta mikawa ma’aikatar harkokin wajen kasar bayan tantancewa da amincewa.
Matakin dai na zuwa ne kwana guda bayan da kasar Jamus, ta sanar da dakatar da galibin ayyukan sojojinta a kasar Mali, bayan da Malin ta ki amince wani jirgin sojin Jamus ya keta hazonta.
Mali dai na bukatar Jamus data bi sabon tsarin.
A ranar 14 ga watan Yulin da ya gabata ne gwamnatin Mali, ta sanar da dakatar da tsarin karba-karba ba sojojin MDD, dake aiki karkashin tawagar Minusma a kasar, yan kwanaki bayan da Bamako ta ce ta kama sojoji 49 na kasar Ivory Coast wadanda ta ce sun shiga kasar ba tare da izini ba.