Mahukunta a Rasha sun bayar da umurnin rufe dukkanin ma’aikatu da kuma wuraren kasuwanci daga ranar 28 ga wannan wata zuwa 7 ga watan gobe a birnin Moscow a daidai lokacin da annobar korona ke ci gaba da hallaka jama’a.
Rasha na ci gaba da samun karuwar alkaluman wadanda ke harbuwa da cutar covid-19 cikin fiye da mako guda, dai dai lokacin da nau’in cutar da aka bayyana da Delta ke barazana a wasu sassan kasar .
A wani labarin nadaban gwamnatin Sudan ta Kudu ta yi watsi da rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ke zargin manyan masu mulkin kasar da wawashe miliyoyin daloli daga asusun gwamnati.
Hukumar ta Kare hakkin dan Adam din ta yi gargadin cewa satar na iya lalata tsarin zaman lafiya da tuni ya kasance mai rauni a Sudan ta Kudun, kasar da har yanzu ke fafutukar murmurewa daga yakin basasar shekaru biyar da tayi fama da shi, bayan samun ‘yancin kai a shekarar 2011.
Sai dai ministan harkokin cikin gidan Sudan ta Kudu Martin Elia Lomuro, ya yi watsi da rahoton, wanda ya bayyana a matsayin wata makarkashiyar hukumomin kasa da kasa ga zaman lafiyar kasar.
Lomuro ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa hukumomi ire-iren na kare hakkin dan adam da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya ba sa kaunar ci gaban Sudan ta Kudu, hakan ya sa suke kirkirar rahotannin karya a fannoni daban daban, musamman kan rashawa da kuma hakkin dan Adam.