Za a haramta amfani da cokali da farantin soso a Ingila
Gwamnmati a Ingila ta tabbatar da cewa za ta haramta kayan cin abinci waɗanda ake amfani da su sau ɗaya ana jefarwa, kamar cokali da farantan soso.
Ba a san yaushe ne harmacin zai fara aiki ba, amma hakan na zuwa ne bayan irin wannan yunƙuri a yankunan Wales da Scotland.
Sakatariya mai kula da harkar muhalli, Therese Coffey ta ce za a yi hakan ne saboda a kare muhalli domin amfanin al’ummar da za ta zo nan gaba.
Masu hanƙoro sun yi maraba da shirin, sai dai sun buƙaci a ɓullo da ƙarin hanyoyin rage amfani da robobi.
Alƙaluman gwamnati sun nuna cewa ana amfani da kwanukan cin abinci na soso guda biliyan 1.1, da cokulla da wuƙaƙen robar sama da biliyan huɗu a ƙasar, cikin kowace shekara.
Ba kasafai ba ne sharar robobi takan ruɓe ba, inda take zama a cikin shara tsawon shekaru.
Duk da kwanuka da cokulan soso kan taimaka ta ɓangaren tsafatar abinci to amma takan ƙare a matsayin shara, inda takan lalata ƙasar noma da rafuka.
Matakin gwamnatin na zuwa ne bayan jerin tattaunawa da masu ruwa da tsaki, kuma za a wallafa matakin ne a ranar 14 ga watan Janairu.
Alƙaluma sun nuna cewa a ƙasar ta Ingila kowane mutum na amfani da aƙalla farantin cin abinci na roba guda 18 da kuma cokula da wuƙaƙen cin abinci 37 a kowace shekara, inda kashi 10% na irin waɗannan robobi ne kawai ake sake sarrafa su.