A yayin wannan ganawa bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da suka shafi ayyukan kafofin yada labarai na kasashen musulmi da kuma ayyukan da suke gudanarwa na wayar da kan al’umma.
Babban malamin na Azhar da kuma shugaban cibiyar kula da harkokin gidajen radiyo na kasashen musulmi sun cimma matsaya kan gudanar da taro na kasa da kasa na gidajen rediyon kasashen kasashen musulmi, musamamn na kur’ani.
Babbar manufar taron dai ita ce kara fayyace muhimman ayyuka da suka shafi sadarwa a kasashen musulmi, inda masana za su gabar da bayanai kan hakan
Baya ga haka kuma sun cimma matsaya kan bayar da horo na musamman dangane da ayyukan kafofin yada labarai an musulmi, wanda cibiyar Azhar za ta dauki nauyinsa.
An kafa cibiyar kula da harkokin gidajen radiyo na kasashen musulmi zaman taron karo na 6 na kungiyar kasashen musulmi ta OIC a shekara ta 1975, kuma wannan cibiya tana karkashin kungiyar kasashen musulmi ne.
A wani labarin na daban Jaridar Guardian ta kasar Burtaniya ta bayar da rahoton cewa, ‘yan sanda sun shiga gudanar da bincike kan sanya wuta da aka yi a kan wani masallaci na musulmi a daren jiya Asabar a garin Manchester.
Rahoton ya ce an sanya wutar ne da dare bayan da musulmi da suke gudanar da harkokinsu a wurin suka bar wurin, inda aka saka wuta da ta yi sanadin jawo gobara a masallacin.
Kafin zuwan jami’an kwana-kwana, wasu daga cikin jama’ar gari da suke wucewa sun fara kawo dauki domin kashe wutar da ke ci a masallacin.
Musulmin da suke tafiyar da lamurran masallacin sun yi godiya ga jama’ar yankin, kan yadda suka nuna damuwa da abin da ya faru da kuma gudunmawar da suka bayar wajen kashe wutar da ke ci a masallacin, lamarin da a cewarsu ya nuna musulmi da al’ummar yankin suna zaune laffiya ne da girmama juna.
A nasu bangaren ‘yan sanda a birnin na Manchester suna ganin cewa harin yana da alaka ne da wasu masu akidar kiyayya da addinin muslunci, kuma sun sha alwashin bin kadun lamarin domin gano wadanda suke da hannu a cikin lamarin domin su gurfana a gaban kuliya.