Za a fara kwaso ‘yan Najeriya daga Ukraine a yau Laraba.
Gwamnatin Najeriya za ta fara ɗebo ‘yan ƙasarta a yau Laraba da suka tsallaka zuwa ƙasashe maƙota daga Ukraine sakamakon yaƙin da ake yi.
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar ta ce ana sa ran rukuni na farko na mutanen za su isa Najeriya gobe Alhamis.
Ta ƙara da cewa zuwa yanzu hukumomi na da adadin ‘yan Najeriya da suka samu shiga Romania da Hungary da Poland da Slovakia. Su ne:
- Hungary – 650
- Poland – 350
- Romania – 940
- Slovakia – 150
Sai dai tun wasu ‘yan Najeriyar da ma baƙaken fata suka koka kan wariyar launin fata da aka dinga nuna musu yayin da suke ƙoƙarin ficewa daga ƙasar.