Yunwa ta kashe wasu yaran Falasdinawa biyu.
A daidai lokacin da ake ci gaba da tsare da zirin Gaza da kuma ci gaba da kai hare-haren sojojin Isra’ila, majiyoyin yada labarai sun rawaito cewa wasu kananan yara Falasdinawa biyu sun mutu sakamakon yunwa.
Yunwa na ci gaba da kashe Falasdinawa kuma adadin shahidan yunwa a Gaza ya kai mutane 27.
A litinin din da ta gabata ne shafin sadarwa na yanar gizo na Aljazeera ya wallafa cewa, wasu yara Palasdinawa biyu sun mutu a asibitin Kemal Adwan da ke birnin Beit Lahia sakamakon tsananin rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin ruwa.
A cewar rahoton, ya zuwa yanzu Falasdinawa 27, wadanda akasarinsu yara ne suka mutu sakamakon rashin abinc.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, musamman arewacin Gaza na fuskantar yunwa, kuma hare-haren Isra’ila sun hana shigar da kayan agaji, kuma daya cikin yara shida a arewacin Gaza na fama da tamowa.
Dalilin da yasa Gaza take halin da take
wannan matsin lamba din da Falasdinawa suke ciki ya samo asaline tun sama da shekara 60 da suka wuce wanda Isra’ilawa sun shigar musu kasa ne ba tare da izinin su ba kuma suka fara gallaza musu saboda fin karfi, hakanne kuma yajawo har bayan shekaru da dama isra’ilawan suka dunga kiran kasar Falasdinu a matsayin kasar su kuma suke kokarin korar mutanan falasdinu daka kasar.
bayan Al’amari ya dau zafi abu yakai har kotun duniya wanda har ta yanke hukuncin a raba kasar gida biyu rabi abawa falasdiwa rabi kuma Isra’ilawa haka a haka aka samu aka dan sulhunta amma duk da haka isra’ilawa ba wai sun hakura bane ba duk da kasar ba tasu bace inda suka dinga bi suna kara girman kasarsu ta hanayar kashe Isra’ilawa da kuma kwace gidaje da garuruwansu.
Falasdinawa sun cigaba da hakuri a hakan, kasantuwar su musulmai ne amma duk da haka aka dinga kiran faladiwa amatsayin yan ta’adda duk da kasancewar kasar suce amma ana ganin Isra’ilawa sune masu hakki sukuma falasdiwa yan ta’adda.
duk a cikin shekarunnan da suka gabata da kuma hakurin da Falasdinawa dukai se a kwanakin baya ne kungiya ta hamas ta dauki babbar fansa akan irin tozarcin da isra’ilawa suke musu.
dalilin hakanne Isra’ila suka rantse kancewa se sunga bayan hamas, abinda aikinsu yake nunawa ba yana nuni ne kan zasu ga bayan hamas ba sedai yana nuni da cewa suna kokarin suga bayan gabadayan falasdinawa.
tun bayan 7 ga watan oktoba ne dai isra’ila suka ta kai hare-here cikin zirin gaza wanda suna kashe yara kananu da mata ne ba wai suna kai hare haren nasu ga hamas bane ba.
a ikrarin netanyahu shine nan da bada dadewa ba zaga bayan hamas toh amma yau sama da kwana 200 kenan haryanzu dai bega bayan nasu ba.
- Duba nan:👉👉Arewacin Najeriya Na Fama Da Sace Sacen Yara