Yemen Ta Bayyana Cewa; Kai Da Komowar Sojojin Amurka A Tekun “ Red Sea” Yana Cin Karo Da Batun Samar Da Zaman Lafiya.
Shugaban tawagar Yamen akan tattaunawar zaman lafiya, Muhammad Abdussalam ya fada a jiya juma’a cewa; Kai da komowar da sojojin Amurka suke yi a tekun; “ Red sea” yana cin karo da batun zaman lafiya a Yemen da Washington ta riya cewa tana goyon baya.
Abdussalam ya wallafa sako a shafinsa na “Twitter” cewa; Abinda Amurkan take yi, wani yunkuri ne na sake karfafa killace kasar Yemen da kuma ci gaba da kai ma ta hari.”
A cikin kwanakin bayan nan ne dai Amurka ta bayyana cewa za ta yi wani atisayen sojan ruwa tare da kawayenta akan tekun “ Red Sea’ domin abinda ta kira karfafa tsaro a yankin da kuma mashigar Babul-Mandab.”
Shi kuwa mataimakin ministan harkokin wajen gwamnatin San’aa Hussain al-Azy, ya bayyana cewa; Tsagaita wutar da aka shelanta tana fuskantar hatsarin rushewa, matukar ba a daina keta ta, kuma ba a bar jiragen ruwa suna kai da komowa cikin sauki ba.”
Saudiyya da kawayenta na yaki suna ci gaba da keta tsagaita wutar yaki da aka shelanta a fakon watan nan na Ramadan mai alfarma, inda a ranar Larabar da ta gabata, jiragen yakinta suka yi shawagi a gundumomi daban-daban na Yemen, tare da kai hari har sau uku.