Jiragen yakin Saudiya da kawayenta sun kai hare-hare kan tashar jiragen sama na birnin San’aa babban birnin kasar Yemen a jiya da yamma, bayan wasu hare-haren da suka kai kan wasu yankuna da dama a kasar.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa jiragen yakin na saudiya sun kai hare-hare kan tashar jiragen San’aa har sau 4. Banda haka sun kai hare-hare kan wasu yankuna a Lardin Sa’ada inda suka kashe mutane akalla 3 .
Haka ma a lardin Ma’arib sojojin na Saudia sun kai hare-hare kimani 20 a lardin. Sai kuma a lardin Hajja sun kai hare-hare har 12 a arewacin Lardin. Sannan sun kai wasu 7 a lardin Juba. Wannan ba shi ne karon farko da kawancen Saudiya suka hare-hare kan tashar jiragen sama na Sana’aa ba.