Yemen; Gwamnatin Kasar Ta Shimfida Sabbin Sharudda Na Sake Tsawita Wuta.
A ranar 2 ga watan Augusta mai kamawa ne
dewa juna wuta tsakanin gwamnatin kasar Yemen da kuma kasar Saudiya da kawayenta, amma gwamnatin kasar Yemen ta ce tana da sabbin sharudde na kara tsawaita tsagaita budewa juna wutan. Ganin yadda bangaren saudiya da kawayenta suka ki aiwatar da dama daga cikin abubuwan da aka kawo a cikin yarjejeniyar wacce MDD ta samar a ranar biyu ga watan Afrilun wannan shekara.
Tasahr talabijin ta almasira ta kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta nakalto Ali Al-Quhoum wani mama a kwamitin harkokin siyasa na kasar yana cewa tun yanzun wasu kafafen yada labarai sun fara maganar a tsawaita budewa juna wuta a yakin na Yemen.
Wannan duk da cewa bangaren sauda sun ki aiwatar da cikekken yarjejeniyar , wadanda suka hada da barin jiragen su tashi su sauka a mtashar Jirage ta San’aa da kuma barin jiragen ruwa su isa tashar jiragen ruwa na Al-Hudaita, amma bangaren saudiya suna sabawa wadannan lamura.
Sauda da dama sun kama jiragen ruwan daukar mai zuwa hudaida sun tsare sannan bas a barin jiragen sama su sauka a yemen kamar yadda aka cimma. Don haka a wannan karon akwai sharudda idan saudiya da kawayenta basu cika suba ba za’a tsawaita yarjejeniyar ba.