Kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan houtsi a Yemen, ta shirya ganin wani mumunan martani idan ba ta kawo karshen goyan bayan da take baiwa kawancen yakin da Saudiyya ke jagoranta kan kasar ba.
Wani mamba a kungiyar ta Ansarullah, mai suna Mohamed Al-Bukhaiti, ya bayyana a wata hira da tashar talabijin ta Al Jazeera cewa ‘’ akwai mummunan martani da Hadaddiyar Daular Larabawa za ta gani idan ba ta tsame hannunta ba daga kai hare hare kan Yemen ba.
Furucin nasa dai na zuwa ne ‘yan sa’o’I bayan da kungiyar ta Ansarullah ta ce ita ce ta kai hare haren a ranar Litini a birnin Abou Dhabi na Hadadiyyar Daular Larabawa a matsayin maida martani kan hannun da Hadadiyyar Daular Larabawa ta ke da shi a cikin kawancen yakin da Saudiyya ke jagoranta kan kasar ta Yemen yau sama da shakaru shida.