Shafin yada labarai na jaridar Al’ummah ya bayar da rahoton cewa, a yau za a sake bude cibiyar hardar kur’ani ta kasar Libya ta domin ci gaba da karatun harda, bayan kwashe tsawon lokaci cibiyar tana a rufe.
Rahoton ya ce tun akwanakin baya ne aka bayar da umarni ga dukkanin malamai da dalibai da su dawo domin ci gaba da karatu, bayan daukar dukkanin matakan da suka dace domin hada yaduwar cutar corona, amma yau ake sa ran sake bude makarantar domin ci gaba da karatu kamar yadda aka saba a baya.
An dai rufe cibiyar ne tun bayan bullar cutar corona fiye da shekara guda da ta wuce, inda a halin yanzu aka sanar da cewa cibiyar za ta dawo domin ci gaba da ayyukanta.
Babbar cibiyar hardar kur’ani ta kasar Libya dai tana daga cikin manyan wurare na ilimi da aka gina tsawon daruruwan shekaru wadda take ci gaba da ayyukanta daga birnin Misrata da sauran yankuna na kasar ta Libya.
Kasar libiya dai tana cikin kasashen da suka shahara da karantarawar alkur’ani kafin na samu yakin basasa a kasar wanda yayi sanadin kashe tsohon shugaban kasar Muhammad Ghaddafi kuma sojojin amurka suna mamaye lunguna da sakunan kasar ta libiya wanda daga wannan lokacin ake ta samun tashe tashen hankula a kasar.