Shin sabon nizamin duniya na shirin samuwa ne? Masu nazartar lamurran siyasar duniya na cewa shiga tsakanin da chana tayi tsakanin Iran da Saudiyya wadanda manyan abokan hamayya ne faffadar alama ce ta canjawar nizamin duniya.
Kokarin Chana domin shiga tsakanin Iran da saudiyyan a gannin masana siyasar duniya hakan na zaman faffadar aama da take nuna canjawar nizamin gudanarwar duniya.
A lokacin tattaunawar da aka gudanar ranar juma’a a birnin pekan tsakanin Saudiyya da Iran kasashen sun amince su sake dawo alakar su ta diflomasiyya, kuma su sake bude “embasssy” dinsu a kasa da watanni biyu, a wannan yarjejeniya Chana ta jaddada batun girmama ‘yancin cin gashin kan kasashe da kuma gujewa shiga sabgogin cikin gida na kasashe.
Rawar da kasar Chana ta taka a matsayin ‘yar shiga tsakanin manyan makiyan yanki kafin fitar da wannan labari a boye ne, karanta hadari da kuma sakamako mai tsoka ga Chana.
Kasashen biyu na yankin tekin farisa a shekarar 2016 ne dai lokacin da Saudiyya ta kashe daya daga cikin manyan malaman shi’a, kasashen sukayanke alaqoqin su, sa’annan masu zanga zanga a Iran suka kai hari ga wuraren wakilcin diflomasiyya na Saudiyya ya kara rura wutar rigimar kasashen biyu.
Tattare da hakan rigimar “Geopolitic” tsakanin kasashen biyu yana komawa shekaru gomomi da suka gabata, duk kasashen biyu a yawancin yankunan gabas ta tsakiya sun fada tankiya domin kowacce takan taimakawa masu goyon bayan ta, wannan ma ta wata hanyar ya kara sanya kasashen sun tsaya a gaban juna.
A yemen a dai dai lokacin da yaki ke cikin shekarar sa ta takwas, Ansarullah suna samun taimako ne daga Tehran, a dai dai lokacin da Riyadh ke jagorantar ayyukan soji domin taimakon gwamnatin yemen.