Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, Hunain Ashraf Abulainain Muhammad yarinya ce mai larurar gani wadda ta hardace kur’ani mai tsarki tun tana da shekaru 7 da haihuwa a kasar Masar.
Wannan yarinya tun bayan haihuwarta da ‘yan watanni ne Hunain ta samu matsalar ciwon daji, wanda ya yi sanadiyyar har ta rasa idanunta tana da watanni 9 a duniya, amma da taimakon Allah ta samu sauki.
Tun tana karama mahaifanta suke koyar da ita karatun kur’ani, a lokacin da ta kai shekaru 7 da haihuwa ta kamala hardar kur’ani mai tsarki baki daya.
Baya ga haka kuma wannan yarinya ta shiga gasar karatun kur’ani mai tsarki sau 20, kuma a kowace gasar ita ce take zuwa ta daya a bangaren hardar kur’ani mai tsarki.
A wani labarin na daban shafin jaridar Sadl Balad ya bayar da rahoton cewa, a jiya Allah ya yi wa sheikh Khamis Jabir Saqar babban malamin kur’ani a kasar Masar rasuwa yana da shekaru 68 a duniya.
An haifi shehin malamina shekara ta 1953 a garin Damnahur ad ke cikin gundumar Buhaira a kasar ta Masar.
Ya yi karatua wajen manyan malamai na lokacinsa, kafin daga bisani kuma ya shiga jami’ar Azhar, inda a cikin kankanin lokaci ya shahara a cikin jami’ar saboda kwazonsa.
Ya koma ya ci gaba da karantawa a jami’ar Damnahur a bangaren addini, kafin daga bisani kuma ya zama shugaban bangaren bincike kan rubutattun kur’anai a jami’ar Azhar a tsakanin shekarun 2003 zuwa 2007.
Sheikh Jabir Saqar cibiyar azhar ta nada shi a matsayin babban daraktan cibiyar kula da lamurran kur’ani na lardin Buhaira baki daya, kuma ya rasu yana a kan hakan.